Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya kan rasuwar Sheikh Yusuf Ali

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a safiyar ranar Litinin, yana da shekaru 73 a duniya.

Shugaban ya aike da saƙon alhini zuwa ga iyalai, ɗalibai, da kuma mabiya wannan malami da ke Kano, da ma Masarautar Gaya wanda wannan malami ke kan karagar Sarkin Malamanta a lokacin rayuwarsa.

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyar ne ta hannun mai magana da yawunsa, wato Ajuri Ngelale.

Ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban abun alhinin da ya karaɗe muryoyin jama’a a faɗin ƙasar nan, duba da irin ɗimbin mabiyan da marigayin ke da su musamman ma mabiyan ɗarikar Tijjaniyya a ciki da wajen Nijeriya .

“A matsayinsa na mai koyarwa, sha’iri, masanin shari’ar Musulunci da tsirrai, kuma uwa uba malamin addinin Islama, Sheikh Yusuf Ali ya yi tasiri ga dimbin jama’a a tsawon rayuwarsa wadda ya sadaukar da ita kacokan wajen neman ilimi da yada shi” in ji Shugaban.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da almajiran marigayin da kuma gwamnatin jahar Kano da al’ummar jihar da ma ɗaukacin Musulmin Najeriya bisa wannan rashi da aka yi ya na mai addu’ar Allah ya jikan Malamin.