An kammala ɗaukar shirin fim ɗin ‘Princess Of Galma’

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A ƙarshen satin da ya gabata ne aka kammala ɗaukar shirin fim na Turanci mai suna ‘Princess Of Galma’ wanda aka shafe tsawon kwanaki 12 ana gudanar da shi.

Shirin wanda kamfanin da ya saba shirya finafinan Turanci a Kannywood na Jammaje Productions ya ɗauki nauyin shirya shi kuma aka yi aikin sa a cikin garin Kano a wannan lokacin, kuma ƙwararren darakta Galadima Muhammad ne ya bayar da umarni yayin da jarumai irin su Magaji Mijinyawa na ‘Gidan Badamasi’, Ishak Sidi Ishak, Hajara Makama, Faruk Sayyadi, Mustapha Musty, Zainab Bichi, Aisha A Musa, da sauran jarumai da dama suke cikin aikin.

Babban furodusan fim ɗin Malam Kabiru Musa Jammaje, ya bayyana aikin fim ɗin ‘Princess of Galama’ da cewa shi ne aiki mafi tsari da kuma kyawon yanayi da ya yi jagoranci a wannan shekara, domin an fara aikin cikin nasara kuma an kammala shi cikin jin daɗi, sauran waɗanda muka yi aikin tare kowa yana cike da farin ciki.

Ya ci gaba da cewa, “Duk da wannan fim ɗin ‘Princess Of Galma’ mun yi shi ne kamar yadda muka saba shirya finafinai na Turanci a masana’antar Kannywood, domin inganta finafinanmu yadda zai yi daidai da yadda a ke gudanar da finafinai a duniya, amma dai wannan shirin da muka yi masa na daban ne. Don haka ne ma a duk lokacin da muka tashi shirya finafinai a kamfaninmu na Jammaje Productions mu ke kashe kuɗi sosai domin samar da finafinai masu inaganci. Kuma shi asalin labarin dai na wata masarauta ne ta wani sarki da a ke kiran masarautar da sunan Galma.

Kuma ‘yar sa mace ce ita kadai, don haka sai a ke gudun kada ya mutu ya sara magajii saboda mace ba ta yin mulkin masarautar don haka a ke nema mata wanda za ta aura da zai zama sarkin idan mahaifin ta ya rasu. Amma duk wanda ya zo neman ta ba ta sauraren sa. Sai ya zama a cikin mafarki ta haɗu da wanda take son ta aure har aka yi soyayya aka yi auren duk a mafarki. Don haka mun zo da wani tsari ne da ya zama baƙo a cikin harkar fim ɗin kannywood wanda daman burinmu shi ne, samar da sauyi ta kowanne ɓangare a cikin harkar yadda za ta samu ta ci gaba da bunƙasa.”

Ya ci gaba da cewar “duk da a yanzu an samu sauyi na yin finafinai masu dogon zango. To mu za mu ci gaba da yin masu gajeren zango don nunawa a sinima da sauran dandamalin nuna fim na gidajen talbijin da ma intanet. Manufar mu dai samar da fim mai inganci a Kannywood wanda duniya za ta yi alfahari da shi, kuma muna sa ran zuwa ƙarshen shekarar nan masu kalllo za su kalle shi a babban taron mu na ƙasa da muka saba yi a duk rana 26 ga Disamba, ranar Jammaje wato ‘Jammaje Day’.”

Shi ma Magaji Ibrahim Mijinyawa, wanda ya fito a matsayin sarki a cikin ‘Princess Of Galma’ ya ce, “a gaskiya na ji daɗin aikin wannan fim ɗin, duk da na shafe tsawon shekaru ina fitowa a matsayin jarumi a finafinan Turanci, to shi wannan da yake tsantsar al’adar Ƙasar Hausa a ke nunawa. abin ya burgeni sosai kuma a shirye nake na bayar da duk wata gudunmawa tawa don ganin an samu nasarar wannan aikin, da ma wanda za a yi nan gaba.”

Ita ma jarumar shirin da ta fito a matsayin Gimbiya Nafisa, wato Hajara Makama cewa ta yi ” To ni sabuwa ce a Kannywood, amma dai na ɗan yi wasu finafinai, sai dai babu wanda aka fi ba ni matsayi babba kamar wannan fim ɗin ‘Princess Of Galma’ da na fito a matsayin jaruma, ina alfahari da shi kuma ina fatan fim ɗin zai ƙara ɗaga darajata a duniya. Babban burina dai ‘Princess Of Galma’ ya samu karɓuwa sosai ta yadda ni ma darajata za ta ƙara yawa.”

Galadima Muhammad, shi ne mai bada umarni a fim ɗin, ya shaida mana cewa ” Wannan aikin na ‘Princess Of Galma’ na daban ne a cikin ayyukan da na saba yi na bayar da umarni, don haka na bayar da lokacina bakiɗaya don ganin an cimma nasarar da a ke so a samu a fim ɗin, don haka ne ma ban ɗauki aikin da wasa ba. ina yin iya ƙoƙari na don na ga na yi abin da ya dace wajen gamsar da masu kallo. Kuma Alhamdulillahi tun da muka fara ba mu samu matsala ba, har zuwa lokacin da muka zo ƙarshen aikin. Ina yi wa kowa fatan alheri a game da goyon bayan da suka ba ni, musamman shi jagoran shirin Kabiru Musa Jammaje.”

Zainab Bichi wadda ta fito a matsayin kuyanga a fim ɗin kuwa, cewa ta yi. ” Ka ga dai na saba fitowa a cikin finafinan Turanci har ma na Kudu, amma dai wannan tsarin fim ɗin ya sha bamban da wamda na saba yi, kuma na ji daɗin aikin sosai don haka na yi aikin cikin jin daɗi.”

Babban abin alfahari da mutane dai suka yi ga wannan fim na ‘Princess of Galma’ shi ne, yadda aka kammala aikin cikin nasara, da fatan kuma zai samu karɓuwa a duninya, domin hakan ne zai ƙara daga martabar masana’antar finafinai ta kannywood a duniya, saboda da ta yi fim da yaren turancin da wasu suke yi wa Kannywood kallon da ba za ta iya samar da finafinai da harshen Ruranci ba, don haka wannan ci gaban harkar fim ne da ma Ƙasar Hausa bakiɗaya.

By Editor