
Daga Umar Garba a Katsina
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa bisa rasuwar Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Umaru Musa Yar’adua.
A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, shugaba Tinubu ya nuna alhininsa bisa rasuwar dattijuwar mai shekara 102 a duniya.
Tinubu ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga Sanata Abdulaziz Yar’Adua da ɗimbin iyalan marigayiyar da ma al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.
Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar’adua, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Shehu Musa Yar’adua da kuma Sanatan Katsina ta tsakiya, Abdul’aziz Musa Yar’adua ta rasu ne a ranar Litinin bayan gajeruwar rashin lafiya.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa a kodayaushe za a riƙa tunawa da Hajiya Dada, saboda taimakon al’umma da take yi gami da goyon bayan samar da zaman lafiya da kuma farin ciki a ƙasar nan, saboda haka ne shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiqanta da rahma.
