
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan wasan Super Eagles da ke ƙungiyar Napoli ta ƙasar Italiya, Victor Osimhen ya amince da koma wa ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya a matsayin ɗan wasan aro.
Fabrizio Romano, wanda ƙwararren ɗan jaridar harkar ƙwallon ƙafa ne ya ruwaito a shafinsa na X da facebook inda ya ce hakan na zuwa ne bayan da wakilan Galatasaray suka tattauna da Osimhen a safiyar ranar Litinin.
Adadin da Napoli ta sanya akan ɗan wasan da farko ya kai Euro miliyan 130 wanda daga baya ya nemi kuɗin ya dawo Euro 75, amma hakan bai sa ƙungiyar ta sallama shi ba.
