Zanga-zanga a Abuja saboda ƙarancin fetur

Spread the love

Wasu masu zanga-zanga sun fito a jiya Litinin a babban birnin tarayya Abuja suna masu kira da a kori shugaban kamfanin NNPCL Mele Kyari a dalilin wahalar mai da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Zanga-zangar na zuwa ne daidai lokacin da kamfanin ke sanar da barazanar rashin kuɗi da ke damun shi. Wanda a sanadiyar haka ne, kamfanin ya ce harkokin shigo da man fetur na samun cikas.

Babban lauyan nan mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana ya bayyana cewa wannan matsin rayuwar ya ta’azzara domin ko titi ka fita za ka kula ba ababen hawa sosai saboda tsadar fetur.

Jagoran zanga-zangar Aminu Abbas ya bayyana cewa ya na mamaki ƙasa mai arzikin mai amma ƴan ƙasa na samun mai da tsada kuma a cikin wahala.

Yayi kira da shugaba Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki cewa ya kamata su gaggauta ɗaukar mataki a kan al’amarin domin ƴan Nijeriya su samu sauƙi.

By ukarofi