DAGA MUKHTAR YAKUBU
A daidai lokacin da ake ta kireye kiraye ga hukumomi na tarayya da na jihohi da su rinƙa mayar da hankali wajen bai wa ilimin yara muhimmanci, sai ga shi ita kuma Amina Hassan Abdussalam ta mayar da hankalin ta ne wajen ilimintar da ƙananan yara ‘ya’yan talakawa da iyayensu ba su da ƙarfin biya musu makaranta, in da ta bayar da gidan ta wajen koyar da su domin su tashi da ilimi mai inganci.
A cikin tattaunawar mu da ita Amina Hassan Abdussalam, wadda ƙwararriya ce a fannin koyarwa ta yi mana bayanin dalilin da ya sa ta zaɓi wannan fanni na koyarwa a maimakon ta je ta yi aikin gwamnati har ma ta kafa gidauniyar yantar da rayuwar yara mai suna ‘Assist the Child Education Foundation’ don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatun mu.
AMINA HASSAN ABDUSSALAM: To ni dai sunana Amina Hassan Abdussalam, wacce za a iya cewa mace ce kamar kowa, amma ba kowa ɗin ba. Idan na ce maka kamar kowa ina nufin a hallita ni kamar kowacce mace ce. Amma ta wasu ɓangarori na rayuwa akwai wajen da muka bambanta da wasu mata.
An san ki a fannin gwagwarmayar samar da ilimi ga ƙananan yara ko ya aka yi ki ka zaɓi wannan fannin?
To gaskiya ni farkon alaƙa ta da ƙananan yara ya samo asali ne daga lokacin da ba kammala karatun difloma wadda kuma ba a fannin ilimi na yi ba. Na yi fannin gudanar da mulki ne, amma da tashi neman aiki sai na samu kaina a aikin koyarwa a zuwan ban samu fannin da nake so ba zuwa wani lokaci zan bari. Amma da na fara mu’amala da yara, sai kuma aikin yake shiga cikin jikina, har ta kai shugaban makarantar yake mamakin yadda nake mu’amala da yara har ma na fi waɗanda suka karanci fannin koyarwa, to a lokacin gwamnatin Kwankwaso na farko a 1999 sai aka fito da tsarin duk malaman da suke koyarwa kuma ba fannin koyarwa suka yi ba a karatu, maimakon a kore su an ba su dama su je su ƙaro ilimi a fannin koyarwa duk da a fannin gudanar da mulki na yi difloma da HND ɗina sai na koma na yi sabon digiri a fannin koyarwa. Don haka ina karatun kuma ina ci gaba da koyar da yara. To a nan na ci gaba da nazartar yara da kuma koyar da su, hakan ya sa na fahimci idan ka zauna da yaro ko da na ɗan lokaci ne, sai ka nazarci wasu abubuwan a tare da shi wanda zai taimaka maka ka gane yadda za ka tafiyar da rayuwa da su. To wannan shi ne farkon mu’amala ta da yara, daman kuma tun da na tashi haka haillta ta take na mai son zama da yaran duk har yanzu ba ni da yaran da yawa, amma duk yaron da ya zo wajena sai ka ga mun saba da shi. Kuma hakan ne ya ba ni damar samar da wani ɓangare na koyar da yaran, to ganin yaran sun fara taruwa saboda yanayin gyaran su ta fannin tsafta da kuma masu kulawa da su sai na buƙaci iyaye su rinƙa bayar da ɗan wani abu, amma dai saboda harka ta jama’a wani ya bayar wani ba zai bayar ba.
Haka dai aka ci gaba da tafiya yara suna ta ƙara yawa, har sai nake ganin sun mayar da ni wata mai yi musu rainon yara, domin a lokacin har yara almajirai suna zuwa da yaran unguwa duk nake koyar da su kyauta, saboda ni na yarda cewar babu daƙiƙin yaro, amma sai ka ga yaro an kawo shi iyayen su na cewa ba su san komai ba, ni kuma sai na ce a turo mini ita na tambaye ta menene matsalar da ba ta gane karatun me ya sa ake ce miki daƙiƙiya.
Ita hallita kowa da yadda Allah ya yi shi, wani yana da saurin riƙe karatu, wani kuma sai a hankali to sai na zauna na koyawa yaro, a nan nake gane yaron ba daƙiƙin ba ne . Ni a haka nake buɗewa yaro kwakwalwarsa har ma iyayen za su zo suna ta mamaki. Da haka aka yi ta tara mini yara ina koyar da su, duk wanda ya kawo yaron sa ya ji ya iya karatu sai ya sanar da wani, shi ma ya kawo nasa, har ya zamana iyayen ma da suke da halin da za su kai ‘ya’yansu makaranta mai tsada, sai su turo mini su.
To wannan ya sa na fuskanci ƙalubale, saboda ba domin su ba na buɗe koyarwar.
Kuma sai ka ga almajiri ya zo ya ce shi yana son ya yi aikin gida, amma uwar daɗinsa ta ce bai iya karatu ba idan an rubuta masa abin da zai sayo ba zai gane ba, don haka yana son a koyar da shi, to haka su ma na rinƙa koyar da su almajiran, duk da su ma na samu matsala sosai da su almajiran, amma dai haka na ci gaba da koyar da su.
A yanzu kina da gidauniya ta koyar da ilimi mai suna ‘Assist the Child Education Foundation’. Shekarar ta nawa, kuma ya aka yi ki ka samar da ita?
To ita harkar gidauniya yadda na fara ta kamar yadda na faɗa maka ne yadda na fara da wannan yaran, to sai ya zamana duk yaron da ya samu ilimi sai a zo a yi godiya, sai kuma a ɗauki sababbi. To sai na ga cewar idan waɗanda Allah ya hore musu za su iya ɗakko malami ya koyar da yaransu, ai bai kamata ma a ce an kawo mini waɗannan yaran ba. Su waɗannan ‘ya’yan talakawa waɗanda za ka ga yaro ya gama aji shida bai iya komai ba, ko kuma makaranta ta yi musu nisa sannan kuma yaro ya gama bai san komai ba, ko kuma ka ga yaro iyayensa nakasassu ne ko makaho ko dai wata tawaya, sai kuma ka ga yaron yana da sha’awar yin karatun, idan muna yi sai ka ga suna zuwa suna leken mu, sai a kira yaron na tambaye shi me ya sa ba ya zuwa makaranta? Sai ya ce ai shi ne yake yi wa babansa jagora zuwa bara, su ma na samu lokaci na koyar da su. Sannan akwai marayu waɗanda babu masu ɗaukar nauyin su, sai ya zama babu abin da suke yi sai jari bola, ni kuma ina jin baƙin ciki na ga yaro a kan bola yana tsince tsince a ce kuma yana da uwa, na tambaye shi Ina babanka ya ce babansa ya rasu, maimakon a ce yana makaranta kuma ya kasance yana kan bola yana tsince tsince. To a nan gidana nake tara su na ba su ilimin da zan ba su su tafi. Idan yaro ya ce sai ya je ya yi barar abincin da zai ci, sai na ce ya zo duk abin da muka samu ya ci. Wani lokaci ma sai mu haƙura mu ba su.
To da haka har aka zo lokacin Kurona da aka daina zuwa makaranta. Wannan ya sa yaran suka saba da ni, don ba su da wajen zuwa, to da haka duk da ba na so amma haka Allah ya Kaddara sai sun zo, duk da ni ba ni da komai amma sai Allah ya turo su wajena, kuma ba zan iya cewa su tafi ba, ko da na ce su yi haƙuri bacci nake ji su bar ni na huta ba za su tafi ba.
Haka ne ya sa mutane suka ba ni shawarar na mayar da abin ya zama tsarin gidauniya, duk da ina ganin ba ni da ƙarfin da zan yi hakan. Sai wata rana wata ƙawata da muka yi karatu da ita ba ma a garin Kano take da zama ba a Legas take ta ga Ina saka abubuwan da nake a soshiyal midiya, sai ta tambaye ni ko yaya sunan gidauniyar da nake jagoranta ko Ina da rajista?
Na ce ba ni da rajista. Sai ta ce ya kamata duk abin da zan yi na zama ina da rajista. Ita ce ma ta bani kuɗin da na yi rajistar, kuma sai ya zama ba mu da ajin da za mu rinƙa koyarwa, saboda daman a cikin gidana nake koyarwa, domin falon gidana na mayar aji ɗaya, can kuma ɗakin yara na mayar aji biyu, shi kuma ɗakin baƙi na mayar da shi aji uku, sai muka koma ni da yara muna kwana a ɗaki ɗaya. Har ma yar idan sun zo wucewa suke tambayar wai nan makaranta ce ko gida? To su iyayen da nake koyar da yaran su, sai labari ya same su cewa takura kaina na yi nake kwana a ɗaki ɗaya ni da yara. Sai su zo su yi ta godiya wasu ma har da kuka. Don akwai yaran ma da idan aka kawo mana su suna ɗauke ma da wasu cututtuka ni nake samar musu da magani har su warke.
To a wannan saka hotunan da nake a soshiyal midiya ita wannan ƙawar tawa da take Legas ta ga hoton yadda nake koyar da yaran a cikin ɗakunan kwana, sai ta turo mini kuɗin da na kama hayar wajen da nake koyar da yaran a yanzu. Kuma a lokacin da nake yi mata godiya sai ta ce ita ya kamata ta yi godiya, saboda na bata damar ta taimaka, don tana da shi ‘ya’yanta suna karatu a waje kuma ga wasu suna karatu a cikin wani yanayi don me ba za ta taimaka musu ba. Kuma a yanzu maganar da nake da kai kuɗin hayar ya ƙare, amma ba zan iya sanar da ita ba, saboda ina jin nauyin kuma in ce da ita kuɗin hayar ya ƙare, tun da wancan ba tambayar ta na yi ba. Haka dai muke tafiyar da abin, yau mu samu gobe ba mu samu ba, littattafai idan an samu ko bai isa ba haka za mu haƙura mu yi amfani da shi.
Waɗanne irin nasarorin kika samu a game da wannan gudunmawa da kike bayarwa ta fannin koyarwa?
Za mu ci gaba mako mai zuwa.

