Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin kantoman Jihar Ribas, a fadar gwamnati dake Abuja, ranar Laraba. Wannan ya biyo bayan naɗin da aka yi masa ranar Talata, sakamakon ayyana dokar ta-ɓaci a jihar saboda rikicin siyasa da ya yi ƙamari.
A yayin rantsarwar, Tinubu ya jaddada cewa matakin yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da doka da oda a Jihar Ribas, tare da magance rikicin da ya dabaibaye jihar.
A gefe guda, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, Hon. Martins Amaewhule, ya bayyana cewa majalisar ta amince da matakin shugaban ƙasa duk da cewa ba abin da suka nema bane. Ya zargi tsohon gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da rashin mutunta umarnin kotu da aikata ayyuka marasa bin doka, wanda hakan ne ya janyo rikicin siyasa a jihar.
Ya kuma tabbatar wa Tinubu da cikakken goyon bayan majalisar ga sabon mai kula da jihar, tare da alƙawarin bayar da dukkan gudummawar da ake buƙata domin sauƙaƙa aikinsa.
Amaewhule ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance cikin lumana tare da goyon bayan sabon jagoranci, yana mai gode wa mutanen jihar bisa addu’o’i da haƙurin da suka nuna yayin wannan yanayi mai sarƙaƙiya.