Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaba Bola Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya sanya bambancin ƙabilu, addinai da al’adu da ke akwai a Nijeriya ya zama tushen wadata, haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa, domin amfanin dukkan ’yan ƙasar.
Shugaban ya yi wannan addu’a ne a ranar Lahadi a birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya, yayin da yake cin abincin dare tare da mambobin tawagar da suka raka shi, kamar yadda mai magana da yawun shugaban aasar, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa. Tinubu ya bayyana fatan cewa bambancin aabilu, addinai da al’adun Nijeriya zai ci gaba da zama ginshiƙin ƙarfinta da ci gaban ƙasa, maimakon ya zama sanadin rarrabuwar kai.
Ya kuma buƙaci ’yan ƙasar su rungumi fahimtar juna, zaman tare cikin lumana da kuma haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba. “Ya Allah Maɗaukakin Sarki, Ka albarkaci Nijeriya, Ka mayar da bambancin da ke tsakanin al’ummarta ya zama sanadin wadata da ci gaba ga ƙasar baki ɗaya,” inji Tinubu.
Haka kuma, shugaban ya roƙi Allah Ya tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da jituwa a Nijeriya, tare da bai wa shugabannin ƙasar hikima, ƙarfin hali da hangen nesa domin su jagoranci ƙasar zuwa ga ci gaba mai ma’ana da inganta rayuwar al’umma. Ya kuma roƙi Allah Ya shiryar da ’yan Nijeriya tare da kare su, ko a cikin gida ko a ƙasashen waje. Ya yi addu’ar Allah Ya ƙara dankon zumunci da ’yan’uwantaka a tsakaninsu, tare da cusa musu kishin ƙasa, tausayi da son hidimtawa al’ummarsu.
Tinubu ya ce ɗimbin albarkatun da Nijeriya ke da su, na mutane da na ƙasa, tare da basira, ƙirƙire-ƙirƙire da ƙwazon jama’arta masu bambancin al’adu, sun samar da kyakkyawan tushe na gina ƙasa mai wadata wadda kowa zai amfana da ci gabanta. Ya buƙaci ’yan Nijeriya daga kowane addini da ƙabila da su ci gaba da haɗa kai wajen yi wa ƙasa hidima, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa Nijeriya za ta iya shawo kan ƙalubalen da take fuskanta ta hanyar imani, haɗin kai da ƙudurin bai ɗaya.
A wajen taron cin abincin daren, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya sake jaddada goyon bayansa ga shugaban ƙasa, yana mai cewa taron ya ba su wata dama ta daban wajen yin addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Nijeriya. Rabiu ya ce wannan shi ne karo na uku da suke cin abincin dare tare da Shugaba Tinubu tun bayan zuwansu Makka a daren Alhamis ko safiyar Juma’a, lokacin da shugaban ƙasar ya isa birnin.
Ya bayyana cewa tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali ne kan yi wa Nijeriya addu’a da kuma nuna godiya bisa yadda Tinubu ke ƙoƙarin yi wa ƙasar hidima. “Za mu ci gaba da mara wa Shugaban ƙasa baya ta duk hanyar da za mu iya. Kamar yadda kowa ya sani, shugaban ƙasa na matuƙar kishin ƙasar nan. Yana aiki tuƙuru, kuma za mu ci gaba da ba shi goyon baya,” inji shi.
Shi ma Gwamnan Jihar Kwara kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, AbdulRahman AbdulRazaƙ, ya yaba wa shugaban ƙasar bisa ƙoƙarinsa na gina Nijeriya mai haɗin kai da wadata. Ya ce, “Allah ne kaɗai zai iya saka maka da alheri. Za mu ci gaba da yi maka addu’a a kullum, tare da yi wa Nijeriya da kake jagoranta addu’a. Allah Ya ci gaba da ƙarfafa ka wajen yanke shawarwari masu kyau, Ya ƙara maka hikima, jajircewa, ƙarfin hali da ƙarfin guiwa. Allah Ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya.”
A nasa ɓangaren, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya yi addu’ar Allah Ya ƙarfafa shugaban ƙasa wajen gudanar da mulki da tabbatar da adalci ga ’yan Nijeriya, ba tare da la’akari da addininsu ko ƙabilarsu ba.
Sauran waɗanda suka halarci liyafar sun haɗa da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi; Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu; da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum. Haka kuma, akwai Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma mai kula da daidaita ayyukan ma’aikatar, Farfesa Mohammed Ali Pate; Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu; Babban Daraktan Kamfanin Oando, Wale Tinubu; Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Kabiru Masari; da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da wasu manyan baki.
