
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin watanni shida a karo na ƙarshe ga wa’adin Kwantirola-Janar na Hukumar Kwastom NCS, Adewale Adeniyi, lamarin da ya ba shi damar cigaba da jagorantar hukumar har zuwa watan Fabarairun 2027.
Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa, ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, wa’adin Adeniyi na farko da zai ƙare ne a ranar 1 ga watan Agustan 2026, amma a yanzu Tinubu ya amince da masa ƙarin watanni shida domin samun damar kammala wasu muhimman sauye-sauye a hukumar..
Onanuga ya ce, an ɗauki wannan mataki ne da nufin ba Adeniyi damar aiwatar da tsarin National Single Window da kuma tabbatar da nasarar aikin.
Kakakin ya ƙara da cewa, a yayin haka Adeniyi zai yi aiki tare hukumar domin sanya ido akan lamuran jami’anta kan abin da ya shafi ƙarin girma da kuma ritaya ga jami’an da shekarunsu ya kai 60 ko kuma suka yi hidimar shekara 35.
Adeniyi ya fara aiki ne da NCS bayan kammala karatu a Jami’ar Obafemi Owolowo a ƙarshe shekarun 1980s ina ya zama maitaimakin kwantirola a 2012.
