Tinubu ya sauya ranar taron Majalisar Zartarwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya ranar da Majalisara Zartarwa (FEC) ta saba zama daga Laraba zuwa Litinin.

Ministan Labarai, Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka ga ‘yan jarida a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kamma taron majalisar a ranar Litinin.

Taron wanda ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, wannan shi ne karo na biyu da Shugaban ke jagorantar taron tun bayan rantsar da shi a watan Mayun da ya gabata.

Idris ya ce mai yiwuwa taron majalisar ba zai riƙa gudana a-kai-a-kai ba musammam idan babu wani muhimmin abu da za a tattauna.

Kafin wannan lokaci taron ya saba gudana ne a Laraba ta kowane mako inda a yanzu Shugaba Tinubu ya koma da shi Litinin.