Tinubu ya yi tsokaci akan nasarori a tattali, titina, ilimi da lantarki yayin cikarsa shekera uku a mulki

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar shimfiɗa tubalin farfaɗo da tattalin arziƙi da sake daidaita al’amuran ƙasa bayan shekaru uku da hawansa mulki.

Tinubu ya bayyana haka ne a jawabinsa na cika shekara uku cif a mulkin gwamnatinsa a yau Juma’a, 29 ga Mayu, 2026.

Shugaban kasar ya ce lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2023, Najeriya na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki, karancin kudaden shiga, matsalar tsaro da kuma tabarbarewar harkokin gwamnati.

Ya ce, gwamnati ta ɗauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin ceto kasar daga durkushewar tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma gyaran tsarin musayar kudaden waje.

A cewarsa, Nijeriya na kashe kusan Naira biliyan 18.4 a kullum wajen tallafin man fetur kafin cire shi, lamarin da ya ce yana hana zuba jari a bangarorin raya kasa kamar hanyoyi, lafiya da ilimi.

Tinubu ya amince cewa matakan da gwamnatin ta ɗauka sun jawo tsadar rayuwa da wahalhalu ga jama’a, amma ya jaddada cewa sadaukarwar da ’yan Najeriya suka yi ba ta tafi a banza ba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya fi samun karfi idan aka kwatanta da shekarar 2023, yana mai cewa kasuwar hannayen jari ta samu gagarumin ci gaba daga darajar kasuwa ta naira tiriliyan 30 zuwa naira tiriliyan 160.

Ya kuma ce gwamnatin sa na gudanar da manyan ayyukan hanyoyi fiye da kilomita 2,700 a sassan kasar nan, ciki har da titin Lagos-Calabar Coastal Highway da Sokoto-Badagry Super Highway da kuma hanyar Abuja zuwa Kano.

A bangaren mai da gas, Tinubu ya ce gyare-gyaren da gwamnati ta yi sun jawo sabbin jarin biliyoyin daloli tare da bunkasa matatun mai na cikin gida domin rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje.

Game da wutar lantarki, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na kokarin magance matsalolin da suka dabaibaye bangaren tsawon shekaru ta hanyar inganta layukan sadar da wuta da kuma zuba jari a makamashi.

A bangaren noma kuwa, Tinubu ya ce gwamnati ta tallafa wa miliyoyin manoma da iri, taki, injina da hanyoyin samun rance domin bunkasa samar da abinci da rage tsadar rayuwa.

Haka kuma ya ce Asusun Lamunin Dalibai na Nijeriya ya taimaka wa sama da dalibai miliyan 1.5 da kudade sama da naira biliyan 282 domin samun damar ci gaba da karatu.

Shugaban kasar ya ce, gwamnatinsa na ci gaba da gina gidaje masu araha a jihohi daban-daban tare da samar da dubban ayyukan yi ga matasa.

Dangane da tsaro, Tinubu ya ce jami’an tsaro sun kara kaimi wajen yaki da ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka, yana mai cewa an fara samun saukin matsalar tsaro a wasu yankuna.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da hada kai tare da nuna hakuri da fatan alheri ga kasa.

Tinubu ya tabbatar wa ’yan ƙasa cewa gwamnatinsa za ta cigaba da ƙoƙarin ganin an rage tsadar rayuwa tare da samar da ƙarin damarmakin ayyukan yi da bunƙasa kasuwanci a faɗin Nijeriya.

By Babaji