5 ga Yuni za a fara jigilar dawowar mahajjatan Nijeriya, inji NAHCON

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta sanar da lokacin fara jigilar dawo da mahajjatan Nijeriya daga ƙasa mai tsarki, Saudiyya, wanda za a fara a ranar 5 ga watan Yuni, 2026.

Daraktanta na horarwa da bincike, Farfesa Abubakar Abubakar ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa Amirul Hajji na Jihar Kano, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulƙadir a Makkah.

Ya ce, an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace wajen ganin an dawo da mahajjatan Nijeriya gida cikin ƙoshin lafiya bayan kammala aikin hajjin na 2026.

A cewarsa, hukumar da haɗin-gwiwar hukumomin kula da mahajjatan jihohi, masu gudanar da tashoshin jiragen sama da hukumomin Saudiyya, sun ɗauki dukkan matakan da ake buƙata wajen dawo da mahajjatan gida Nijeriya bisa tsari.

Ya bayyana cewa, an tsara jigilar ne domin tabbatar da kauce wa samun jinkiri da cinkoso a filayen jiragen sama don kiyaye walwalarsu har zuwa kammala hajjin.

Haka kuma ya yaba wa matakin haɗin kai da aka samu daga jami’an hajji na jihohi da masu ruwa da tsaki a aikin hajji, yana mai bayyana na bana a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyan tsari a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

Farfesan ya kuma roƙi mahajjatan da su kiyaye dukkan sharuɗɗan da aka gindaya da suka shafi kayayyakinsu, takardun tafiye-tafiye da tsare-tsaren tashi.

Kazalika, ya shawarce su da su cigaba da kiyaye horo da haƙuri, yana mai cewa dawowar tasu cikin nasara ta ta’allaƙa ne da haɗin kan da za su bayar akan al’amarin.

By Babaji