Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Sanata Kabiru Garba Marafa, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar National Democratic Congress NDC a Zamfara, ya yi kira ga masu zaɓe da su zaɓi cancanta a zaɓen 2027, yana mai cewa sakamakon zaɓen shugabanni marasa tasiri zai dogara ne kawai ga masu zaɓe kuma alummar jihar za su ɗanɗana kuɗarsu a hannun shugabannin da ba su dace ba in har suka zaɓe su.
Marafa ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis a Gusau, jim kaɗan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna a jam’iyyar NDC da aka gudanar a babban birnin jihar.
“Ya kamata mutanen Zamfara su zaɓar wa kansu mafita wajen zaɓen shugabannin da suka cancanta ba bara gurbi ba a 2027.”
“Idan suka zaɓi shugabanni marasa tasiri a 2027, za su yi kuka da kansu,” inji Sanata Marafa
Tsohon sanatan da ya wakilci Zamfara ta tsakiya ya ce zaɓen 2027 zai zama lokaci mai mahimmanci ga jihar, wadda ke ci gaba da yaƙi da rashin tsaro, talauci, da kuma raunin ayyukan gwamnati.
Ya ƙara da cewa shugabanci a matakin jiha dole ne ya dogara akan ƙwarewa, gogewa, da jajircewa wajen magance matsalolin mazauna jihar, ba wai akan siyasa ta son rai ko kuɗi ba.
“Wannan zaɓen ba wai jam’iyya alummar Jihar Zamfara za su duba ba, su dubi makomar ‘ya’yanmu, Zamfara ta sha wahala sosai”.
“Dole ne mu zaɓi shugabannin da suka fahimci wahalar mutane kuma suna da ikon samar da mafita,” in ji Marafa.
Ya yi alƙawarin gudanar da kamfen bisa ga batutuwan mayar da hankali kan tsaro, noma, ilimi, da aikin yi ga matasa idan aka zaɓe shi gwamna.
Marafa ya kuma yi alƙawarin gudanar da gwamnati mai haɗaka wacce za ta ba da fifiko ga gudanar da gwamnati cikin tsari mai ma’ana musamman wajen kashe kuɗaɗen gwamnati.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa an gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna a ƙarƙashin ham’iyyar ta NDC cikin lumana kuma an zaɓi Sanata Marafa ba tare da hamayya ba.
