Daga MAHDI M. MUHAMMAD da
SANI AHMAD GIWA
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ƙudurin rage farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa.
Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, 2024, lokacin da ya karɓi baƙuncin Babban Sakataren Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Caca na ƙasa, Tosin Adeyanju, wanda ya jagoranci tawagar gudanarwar hukumar zuwa ziyarar ban girma ga ministan a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.
Wannan ƙuduri ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya suke kokawa da tsadar wutar lantarki a bana bayan ƙarin kuɗin lantarki da kamfanonin rarraba wutar lantarkin suka yi.
A halin yanzu, abokan cinikin masu amfani da rukunin Band A suna da tabbacin samun wutar lantarki aƙalla na sa’o’i 20 a kullum, kuma ana sa ran za su biya Naira 209.5 kan kowane Kilowat a cikin sa’a guda domin gujewa ƙorafin ’yan ƙasa da masana’antu kan tsadar lantarki.
Amma da yake magana a yayin taron, ministan ya ce, ‘’yan Nijeriya za su iya tabbatar da rage tsadar wutar lantarki, tare da ƙoƙarin inganta samar da wutar lantarki a ƙasar.
Adelabu ya yi ikirarin cewa farashin wutar lantarki a Nijeriya ya ragu kaɗan idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Afirka da suka haɗa da Togo da Mali da Jamhuriyar Nijar.
Ya yi nuni da cewa, ƙarancin kuɗin shiga na ƙasar ya kan sanya kuɗin da ake kashewa ga masu amfani da shi, inda ya ce wutar lantarki ta fi ƙarfin sarrafa injinan mai da man fetur ko dizal, musamman ta fuskar hauhawar farashin man fetur.
A wani cigaban kuma, a ranar Alhamis ne Majalisar Dokokin Nijeriya ta samu wasu ƙudurorin zartarwa guda huɗu daban-daban daga hannun Shugaba Bola Tinubu kan yin gyare-gyare a hukumar haraji, ɗaya daga cikinsu shi ne dokar da ke neman sauya sunan Hukumar Tattara Haraji ta Tarayya (FIRS) zuwa Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS).
ƙudirin canza sunan na FIRS kamar yadda yake ƙunshe a cikin wasiƙar da shugabanta, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar dattijai mai taken: “ƙudirin dokar hukumar tara haraji ta Nijeriya (Establishment) wanda a cewar Shugaba Tinubu, na neman soke harajin cikin gida na tarayya. Dokar Ma’aikata (Establishment) mai lamba 13, 2007 da kafa hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Nijeriya, don tantancewa, tattarawa da kuma lissafin kuɗaɗen shiga da za a iya samu ga gwamnatin tarayya.
Sauran dokar garambawul a cikin wasiƙar mai suna: “Mayar da Dokokin Kasafin Kuɗi da Dokokin Gyaran Haraji zuwa Majalisar Dokoki ta ƙasa”, sune (i) Dokar Harajin Nijeriya da ke neman samar da tsarin hada-hadar kuɗi na haraji a Nijeriya;
(ii) ƙudirin dokar kula da haraji ta Nijeriya, wanda ke neman samar da tsayayyen tsari na doka don tabbatar da gaskiya, daidaito da inganci na duk dokokin haraji don sauƙaƙa biyan haraji, rage taƙaddamar haraji da inganta kuɗaɗen shiga.
(iii) ƙudirin hukumar tattara kuɗaɗen shiga (Establishment) wanda ke da nufin kafa hukumar tattara haraji ta haɗin gwiwa, kotun ɗaukaka ƙara ta haraji da kuma ofishin mai kula da haraji don daidaitawa, da sasanta rigingimun da suka taso daga harkokin kuɗaɗen shiga a Nijeriya.
A cewar shugaban, ƙudurin dokar harajin da aka gabatar yana gabatar da fa’idodi masu yawa ga ɗakin karatu, hada-hadar gwamnati da bunƙasar tattalin arziki ta hanyar inganta masu biyan harajin da ke ƙarfafa cibiyoyin hada-hadar kuɗi, da samar da ingantaccen tsarin kasafin kuɗi na gaskiya.
“Ina da yaƙinin cewa ƙudirin idan aka zartar da shi, zai ƙarfafa zuba jari, da bunƙasa kashe kuɗi da kuma ƙara haɓaka tattalin arzikin Nijeriya,” inji shi.
