Tinubu zai tuntuɓi Antoni Janar bayan karɓar ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi kudirin gyaran kundin tsarin mulki na shida, wanda ya tanadi kafa rundunonin ’yan sandan jihohi a Nijeriya, lamarin da ya kusantar da shirin zama doka.

Blueprint Manhaja ta rawaito cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Gbajabiamila ya ce an miƙa wa Tinubu kudirin a hukumance ne a ranar Laraba ta hannun masu ba shi shawara na musamman kan harkokin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, Sanata Basheer Lado da Wasiu Olanrewaju-Smart.

Ya bayyana cewa shugaban ƙasar zai nazarci kudirin gyaran kundin tsarin mulkin tare da tuntubar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, kafin sanya hannu a kansa a wani bikin rattaba hannu na musamman.

A wani ɓangare kuma, Gbajabiamila, wanda shi ne shugaban Kwamitin Aiki na Shugaban ƙasa kan ’Yan Sandan Jihohi, ya ce kwamitin, tare da goyon bayan Kwamitin Ba da Shawarwari kan Manufofi, ya gudanar da tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki da kuma shawarwari a faɗin ƙasar domin samar da daftarin kudirin dokar kula da harkokin ’yan sanda ta ƙasa.

Ya bayyana cewa an miƙa daftarin kudirin ga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya domin tantance ingancin tsarin rubutun dokar.

“Da zarar an kammala tantancewa, Kwamitin Aikin zai sake nazarinsa tare da miƙa shi ga Mai Girma Shugaban ƙasa, tare da rahotonsa, domin ya duba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Shugaba Tinubu na miƙa godiyarsa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai, mambobin Majalisar Tarayya, Magatakardar Majalisar Tarayya, gwamnonin jihohi 36, majalisun dokokin jihohi da dukkan ’yan Nijeriya da suka nuna ƙudurin bai ɗaya na magance ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.”

A baya, Majalisar Dattawa ta umarci Magatakardar Majalisar Tarayya da ya miƙa wa Shugaba Tinubu kudirin gyaran kundin tsarin mulkin da ya tanadi kafa ’yan sandan jihohi domin ya sanya hannu a kansa.

Majalisar ta kuma buƙaci bangaren zartarwa da ya miƙa wa Majalisar Tarayya kudirin dokar kula da harkokin ’yan sanda ta ƙasa domin a yi masa nazari tare da gaggauta amincewa da shi, don samar da tsarin gudanar da ayyukan ’yan sandan jihohi.

Waɗannan shawarwari sun biyo bayan kudirin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Laraba.

A ranar Litinin ne Magatakardar Majalisar Tarayya, Kamoru Ogunlana, ya sanar da cewa dukkan majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin da zai ba da damar kafa ’yan sandan jihohi, wanda hakan ya share fagen miƙa shi ga shugaban ƙasa.

Ya ce amincewar ta zarce ƙa’idar da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, wadda ke buƙatar aƙalla majalisun dokokin jihohi 24 su amince da gyaran, bisa tanadin sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, kamar yadda aka yi masa gyara.

By ukarofi

Leave a Reply