Tinubu zai yi tankaɗe da rairaya a gwamnatinsa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin yin tankaɗe da rairaya wa ma’aikatan gwamnatinsa a ƙoƙarinsa na inganta ayyukansa wa al’ummar Nijeriya.

Shugaba Tinubu na samun matsi daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta APC kan neman ya tsige wasu ministoci da ba sa ayyukansu yadda ya kamata.

A shekarar da ta gabata ne Tinubu ya naɗa kwamitin karɓar rahoton ayyukan ministoci da wasu manyan jami’an gwamnatinsa ƙarƙashin jagorancin Mai bashi Shawara ta musamman kan tsara shirye-shirye, Hadiza Bala Usman.

Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka bai wa muƙami na minista ko mashawarci ko makamancin haka da bai kiyaye aikinsa ba, to za a tsige shi.

A satin da ya gabata ne Tinubu ya maye gurbin Daraktocin hukumomin Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA) da na ƴan sandan farin kaya ta DSS bayan da suka ajiye ayyukansu.

Wata majiya daga ofishin shugaban ƙasa ta ce za a fara gudanar da tankaɗen ne nan ba da jimawa ba.

Majiyar, wacce ba ta amince a bayyana ta ba, ta ce wasu ministocin za a tsige su ne yayin da wasu kuma za a sauya mu su ma’aikatu don inganta ayyukansu.

Ta ƙara da cewa, Shugaba Tinubu na buƙatar ma’aikata da suka fi na yanzu ƙoƙari don cimma manufofinsa na zartar da ayyukan da ya alƙawaranta wa ƴan Nijeriya.

By Babaji