Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar masu mallakar kamfanonin kasuwanci da kamfanonin fasahar sadarwa da makamantansu da ake kira Technology Innovation & Solution Network Initiative (TISNI) ta samar da tsari irinsa na farko ta yadda ɗaliban da suka kammala jami’a da manyan makarantu za su ci gajiyar rubutunsu na kammala karatunsu da ake kira project, wanda shi ne TISNI ta tsara horar da su da tallafa musu ta hanyar jagoranci da wannan rubutun na ɗalibai zai samawa waɗannan ɗalibai aiki na dogaro da kai, kamar dai yadda Hajiya Maryam Abbas Abdulƙadir Bichi, shugabar hulɗa da jama’a da kuma yaɗa labarai ta ƙungiyar TISNI ta bayyana a wurin taron horar da ɗalibai da aka yi a Jami’ar MAAUN da ke Kano a ranar Alhamis ɗin makon jiya.
Haka kuma ta ƙara da ce wa babban maƙasudin kafa wannan ƙungiya a shekara 2023 domin a tattaro kamfanoni da masu ƙirƙire-ƙirƙire domin a taimakawa ɗalibai waɗanda suka gama karatu da kuma tattara abubuwan da suka yi rubutu akan sa a horar da su a tallafa musu domin su ci gajiyar wannan aiki nasu wanda hakan zai taimaka musu wajen zama wani abu a rayuwarsu, domin ta irin wannan hanyar ne aka samu matasa da sauran masu fasaha suka samar da manhajar kafar sada zumunta da sauran manhajoji waɗanda yau ake amfani da su a duniya kuma suka samarwa matasa da saurasu hanyoyin ailkin yi da arziƙi mai yawa kamar yadda malama Maryam Bichi ta bayyana.
Har ila yau ta ƙara da cewa wannan shiri shine na farko da aka zaɓo ɗaliban da rubutun su yake da alaƙa ko sauƙin aiwatarwa domin ya amfane su guda 50 daga wannan jami’a ta MAAU wato Maryam Abacha American University da ke Kano, wanda kuma wannan taro haɗin gwiwa ne da wannan jami’a ta MAAU.
Ta ce za su cigaba da aiki da jami’o’i irinsu BUK, ADUST, KHAIRUN, NWU da kuma manyan makaratu na gaba da sakandire don zaƙulo irin waɗannan ɗalibai da taimaka musu don ganin sun samu aiki da karatunsu ba tare da dogaro da samun aikin gwamnati ba.
A ƙarshe Daraktar hulɗa da jama’a da yaɗa labarai ta ƙunigiya TISNI Malam Maryam ta nemi haɗin kan shugabannin jami’o’i da na manyan makarantu su bai wa wannan ƙungiya domin tallafawa ɗalibai da suka kammala manyan makarantu domin su samu kyakkyawar makoma.
