Tsadar fetur: COEASU ta umarci malamai su koma aiki sau biyu a mako

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (COEASU) ta bai wa mambobinta umarnin taƙaita zuwa aiki zuwa sau biyu a sati har sai gwamnatin Tarayya ta ƙara musu albashi da kashi 200.

Ƙungiyar ta ce, umarnin zai fara aiki ne nan take har zuwa lokacin da za ta gudanar da taron gaggawa domin yanke adadin kwanakin da ya kamata malaman su cigaba da zuwa aiki.

Shugaban ƙungiyar, Dokta Smart Olugbeko ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce duk da cewa ƙarin kuɗin man fetur da gidajen mai suka yi a safiyar ranar Talata zai jefa ma’aikatan cikin ƙunci, za su ci gaba da jurewa, domin suna da ƙwarin gwiwar Gwamnatin Tarayya za ta samar musu da mafita.

“Cire tallafin man fetur da gwamnatin taryya ta yi watanni biyu da suka gabata ya sa an samu ƙarin farashin man fetur da kashi 250, wanda hakan kuma ya haifara da hauhawar farashin masarufi, sufuri da sauran ɓangarorin rayuwar talaka.

“Sai dai muna da yakinin gwamnatin za ta samar wa ’yan Nijeriya musmaman ma’aikatanmu mafita ta hanyar raba tallafi da kara mana albashi,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *