
Daga BELLO A. BABAJI
Tsagin NNPP ƙarƙashin jagorancin Dakta Agbo Major ya tabbatar da korar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Buba Galadima da baki ɗaya tawagar ƴan Kwankwasiyya daga jami’yyar, biyo bayan taronsa na ƙasa da aka gudanar a Jihar Legas a ranar 4 ga watan Fabrairu.
Haka kuma ya tabbatar da zaɓar Dakta Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam’iyya da kuma sababbin mambobin Kwamitinta na Ayyuka na Ƙasa (NWC).
A yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja, ranar Asabar, Dakta Major ya ce jam’iyyar tana ƙoƙarin bin hukuncin Babbar Kotun Jihar Abia inda ta amince da Kwamitin Amintattu ƙarƙarshin jagorancin Dakta Boniface Okechukwu Aniebonam har zuwa lokacin da za a kawo ƙarshen ɓarakar da ke cikin jam’iyyar.
Dakta Major ya kuma ce sun bi hanyoyin doka ne wajen gudanar da zaɓukan jam’iyyar, ya na mai watsi da ikirarin halascin shugabancin ƴan Kwankwasiyya.
Ya ƙara da cewa, taron ya yi sanadiyyar dawowa da asalin bajin jam’iyyar tare da soke wani nau’in da ƴan ɓangaren Kwankwasiyya suka gabatar a baya.
Kazalika, ya ce nan ba da jimawa ba hukumar zaɓe, INEC, za ta sabonta jaddawalin shugabancin jam’iyyar kamar yadda kotun ta bada umarni.