Tsakanin hukumar tace fina-finai, Afakalla, Majalisar Dokokin Kano da ‘Yan Kannywood

Daga HAMISU LAMIDO IYANTAMA

Da farko dai a fahimtata da kuma ɗan ilmin da Allah Ya ba ni daidai gwargwado a kan wannan harka ta fim, ban ga laifin hukumar da ta dakatar da nuna waɗannan halaye a fim ba. duba da bibiyar yadda ita kanta Gwamnatin Tarayya ta kafa hukumomi masu kula da wannan ɓangare ta hanyar inganta sanaar da masu yin sanaar, gwamanti ta yi tanade-tanade masu yawan gaske a kan hakan.

Amma saboda rashin bibiya ko kuma in ce ƙarancin bincike a kan tanadin da waɗannan hukumomi suka yi mana tun kafin mutum ya fara wannan sanaa su ne dalilan da suka janyo a duk lokacin da wata hukuma ta bijro da wata doka domin kawo gyara, ko kuma da ma da akwai wannan doka amma ana son a inganta ta to, daga jin haka sai ka ji an fara cece-kuce! Kowa na faɗar raayinsa wanda wannan ra`ayi nasa ya saɓawa dokar, amma fa shi mai yin ƙorafin yana ganin shi ke da gaskiya alhali ba haka ba ne.

Akwai kundin tsarin yadda Gwamnatin Tarayyar ƙasa ta rubuta hanyoyin da duk wani mai son shirya fim a wannan ƙasa zai bi domin gudanar da harkokinsa yana nan cikin (National Film Policy), wannan kundi ya hana nuna abubuwa da dama waɗanda suka jibinci fito da tsirarar aikata wasu laifuka manya da ƙanana a fili. Wannan kundi ya haramta nuna abuabuwan da ake ta cece-kuce a kai. Amma saboda sakaci na hukumomin da alhakin ya rataya a kansu da son zuciya da rashin zuba ƙwararru su zamo su ne masu kula da wannan ɓangarori, ya janyo mafiya yawan masu shirya film suke ganin abun kamar wani sabon abu ne. Babu sabunta cikin dokonkin da hukumar tace fina-finai ta jahar Kano ta yi bisa wannan batu da muke ganin ba a kyauta.

Yana da kyau ‘yan’uwa masu wannan sana’a su ƙara faɗaɗa binkice da neman ilmin abunda ba su san shi ba. Kuma su dinga yi wa dokoki da ƙa`idoji sabbi da tsoffi kallo da idon basira.

Mene ne laifi don an ce kar mu fito ƙarara muna aiwatar da laifuka a zahiri, a halin da ƙasarmu ta tsinci kanta na rashin tsaro da sauran nau’uka na ta’addanci kala-kala. Ai ya kamata a ce ko cewa aka yi mu dakata da shirin film a yanzu idan har dakatarwa za ta kawo mana sauƙi cikin al’amura to mudakata ɗin.

Idan ni ɗan film ko mai shirya film na yarda da cewa mutane na fa`idantuwa idan sun kalli film ɗin mu to, dole kuma mu yarda cewa idan muka saka saɓanin hakan wasu za su iya koyon aikata sharri ko wasu su koyi rashin tarbiya. Ba kowa ba ne ya san cewa don ka nuna aikata laifi da masu aikata laifin a cikin film kafin ka zo ka nuna sakamakonsu a ƙarshen fim ba sai nadiran ba. Ba kowa ba ne ya san cewa kowane film akwai irin rukunin mutanen da aka shirya wa film ɗin. Haka ma ba kowa ba ne ya san cewa hukumomin tace finai-finai suna da ‘Classifications’ na shekaru ga masu kallon fina-finai.

Da yawanmu sun sani cewa duk wani fim da aka shirya akwai rukunin shekarun mutanen da ake so su kalla kuma an yi fim ɗin ne domin su. Saboda haka, ƙaranci masaniyar haka ta sa masu kallon lamarin ba a dai-dai ba suka fi yawa.

Amma fa a wani ɓangaren, dukkan mu mun san cewa shiriya ta Allah ce amma tarbiyantarwa ta mutum ce. Allah kaɗai ke bada shirya, Shi yake shiryar da wanda Ya so, Ya ɓatar da wanda Ya so.

Tun kafin fina-finan Hausa su haɓaka babu irin fim da ba mu gani ba da ‘yan daba da shaye- shaye iri daban-daban da sace- sace, fina-finai irin na Daku amma mu ba mu koya ba. Allah bai so mu ɓata ba ta dalilin kallon fim.

Idan fim ɗin Hausa na ɓatarwa to, na ƙasashen ƙetare ma na ɓatarwa. Duk da cewa fa mun yarda da cewa shiriya ta Allah ce ba waninSa ba. To, ina imaninmu yake a nan kenan? Haƙƙinmu ne mu yi ƙoƙari mu nuna muhimmacin aikata alheri kuma mu nuna illar aikata sharri.

Tun ran gini, tun ran zane! Afakalla ya ɓata rawarsa da tsalle ta hanyar ɓatawa da mutane da dama da suka fito daga wannan masana’anta da yawan mutanen da suka taimake shi a rayuwa da ‘yan-ga-ni-kashe-ninsa sun ɓata, har da ni kaina.

Afakalla ya janyo na yi asarar kuɗaɗe masu yawan gaske, kama daga kwamitin gyaran kasuwa da hukumar ta kafa kuma aka ba ni shugabancin kwamitin da kuɗaɗe na ko kuma in ce kuɗaɗen aljihunmu muka aiwatar da wannan kwamiti.

Babu yadda za a ce hukuma ta kafa kwamiti amma ba a ba su kuɗin zama ko zirga-zirga da sadawar da buga takardu ba. Amma saboda ganin shi namu ne kuma mun yi zaton dukkanmu za mu amfana da ƙudirin da aka ɗora mana nauyi daga ƙarshe haka muka ɓaɓe.

Yan’uwa! dangantaka ta Afakallah da sanin ko ni waye a ɓangaren shirin fim ta yi ƙarfin gaske, duk da alaƙata da Afakallahu amma ya riƙe mun ‘certificate’ har yanzu bai ba ni ba, fim ɗin da na kashe wa milyan N1 da dubu 800 mai suna (Wuta A Maƙera) saboda wani dattijo ya zagi wani yaro don yaron ya yi ƙarya Dattijon ya ce yanzu wannan shegen yaron cewa ya yi da ku ɗan uwanta ne? Sai aka ce sai na cire shegen yaron, ni kuma na ce masa bisa zamantakewa ta Malam Bahaushe, iyaye ko manya suna zagin na lasa da su cikin fushi.

Toh har yau shiru kakeji tun 2018. Kuma fina-finan nan da na yi Afakalla ya ƙarfafa mun gwiwa da na yi su har faɗa wa mutane yake yi cewa shi ya ce na yi kuma na ɗebo kudina suna ajiye a ‘account’ na zuba ga su nan jibge gabana guda 5 kullum sai zaman makoki nake yi, ita kasuwar ba ta gyaru ba ballantana in kai ko kuɗina sa dawo. Afakallah wallahi ya cutar da ni fiye da tunaninku. Mutum ne da bai san yadda zamantakewa take ba.

Shin maakatan tace fina-finai na Kano sun fi na ƙasa kwarewa ne da har 'National' suka kalla suka yaba suka ba ni 'certificate' amma na jiha suka ce ban iya ba, yaran da tun kafin a haifi wasunsu na gama sanin mene ne dokoki da ƙaidodin yin fim, kuma na yi fina-finai ban taɓa kai fim an ce mini ga gyara ba.

Na yi ƙorafi ya ce min laifin daraktana ne. Abun tambaya a nan shi ne, ni ne na kawo films censors ba Director na ba. Yanzu haka za mu dinga rayuwa muna daƙile juna?
Amma duk da haka, idona ba zai rufe ba idan maganar gaskiya ta zo zan faɗa koda ba zan samu goyon baya ba.

Afakalla ka yi ƙoƙari ka gyara mu’amalarka da ‘yan-ga-ni-kashe-ninka. Da yawan su suna ganin kana yi mana dingushe da dungu har da ni a ciki kuma ka san da haka. Yadda kake kiran sunan Allah haka mu ma muke kiran sa inda aka zalunce mu to, Yana nan Yana gani.

Kar ka manta matattakalar wannan masana’anta ka bi ka tsinci kanka a inda kake ba don ka fi kowa ba, Allah Ya yi maka. Amma a ce kowa sai Allah wadai. Ni dai ban ji daɗin rashin kyakkyawar alaƙarka da mokamarka ba wadda ita ce Kannywood.

Koda kana ganin ka samu duniya ka haye ba za ka dawo cikinmu ba, ka tuna akwai ranar ɗaurin aure, mutuwa ko suna. Ka tuna akwai ranar jaje da ranar murna ai za mu haɗu domin haka.

‘Yan’uwa abokan sana’a, mu sani cewa wannan kujera ta hukumar tace fina-finai musanman ta kano tana da hatsarin gaske, kowa aka bai wa da wuya a gama lafiya da shi, saboda kujera ce da take kare dokokin gwamnati kuma doka ce ta yi wannan hukuma. Afakalla ma’aikacin gwamnatin ne, albashi yake ɗauka duk wata da sauran su. Saboda haka, alaƙarmu da shi ita ce mu yi abun da bai saɓa mata ba, da daɗi ko ba daɗi. Duk wanda ya bi doka zai zauna lafiya. Mu ci gaba da yin fina-finai masu inganci. KannyWood na da ƙwararru da matasa masu hazaƙa. Ku kalli ƙudirin dokar ku yi fim bisa dokar za ku iya kuma mutane su kalla su gamsu. Na tabbata da hakan zai yi.

Haka kuma ‘yan’uwa masu sana’a, a dinga kallon abubuwa da idon basira. Idan har za ku yi wa Afakalla ihu da surutai a kan wannan ƙudiri, to, me ya hana ku ku yi wa Shuganban Hukumar Tace Fina-finai na Ƙasa wanda shi ne ya fara tabbatar da wannan ƙudiri sai dai shi bai hana riƙe makamai ko hana shaye-shaye ba da sauransu ba, ya ce dai lalle ba za su lamunci fifita masu laifi da ba su nasara ba ko kuma kambama masu laifin a cikin fins-finai ba da sauran su.

Ina zaton daga wannan jawabi ne da shugaban hukumar tace fina-finai na ƙasa ya yi shi kuma Afakalla ya aro ya kuma zo da nasa tsarin wanda bai yi wa ‘Yan Kannywood daɗi ba. A ilmin aiwatar da fim akwai rashin fahimta idan har aka ce a daina nuna masu laifi ta yadda suke aikata shi laifin, idan kuwa hakan ta tabbata to, za kuwa a daina nuna hukuncin da duk wani laifi da aka aikata kuma an daina nuna muhimmanci aikin ɗan sanda, ko soja, ko alƙali kenan a cikin fim, dole sai an aikata ba daidai ba sannan za a nuna hukuncin wanda da rataya ga mai laifin a kotu ko wajen jami’an tsaro.

Fim yana da dokoki da tsarin yadda ake tafiyar da shi. Haka ala’adunmu, haka addininmu, haka kuma ita hukuma.

Dole ne mai shirya fim ya yi ƙoƙari ya bai wa kowannensu haƙƙinsa ta inda zai gamsar da mai kallo.
Wannan doka da aka ce Afakalla ya faɗa a kafafen jaridu yaushe Majalisar Jihar Kano suka zauna suka tabbatar da ita? Wane ɗan majalisa ne ya gabatar da wannan ƙudiri? Zama nawa aka yi wajen miƙa wannan ƙudiri a majalisar?

Idan kuma majalisa ce ta amince da hakan, muna buƙatar sabon kwafin dokokin hukumar domin mu karanta. Dole dai sai majalisa ta saka hannu a wannan doka kafin shugabanta ya fito ya fara yaɗa wa duniya.

Hukumar tace fina-finai dai ta jihar Kano Majalisa ce ta zauna ta kafa ta ta yi mata dokoki, wani mutum shi kaɗai tilo bai isa ya kafa doka ba shi kaɗai sai dai majalisa. Ko kuma ni ne ban gane ba. Idan ni ne ban gane ba to, ina neman sani, a sanar dani. Ko kuma da ma wannan doka tana cikin kundin tsarin hukumar?

Wannan fahimtata ce kowa da tasa fahimtar. Kuma ban yi wannan rubutu don in ɓata wa wani ba sai don neman mafita ko gyara. Allah sa mu gane.

Iyantama shi ne Shugaban Kamfanin Iyantama Multimedia kuma yana ɗaya daga cikin manya a masana’antar shirin fim ta Kannywood