Tsakanin Sakkwatawa da Gobirawa

Spread the love

Daga FARFESA IBRAHIM MALUMFASHI

Zuwa ga Rabiu Isah Hassan da Bichiia Maisango,

Dangane da post da na yi domin amsa tambayar wani ɗalibi game da Hausawa Zalla, na taɓo batun Sakkwatawa da Gobirawa ne da ‘gangan’ domin mu faɗaɗa tunani game da al’amarin.

Ba wani mai bincike ko nazari ko da kuwa ‘mahaukaci’ ne da zai ce ba al’ummar Hausawa a doron ƙasa ko kuma ba su da al’adu da tadoji ko kuma ba ƙabila ba ce, taron gambiza ne, babu, sai dai ƙila bincike ko nazari na son rai.

Kamar yadda na sha faɗa, ni ba masanin tarihi ba ne, ɗalibin tarihi ne, mai neman sani ne, shi ya sa kullum nake yawan tambayoyi da neman amsoshi.

Batun ko Sakkwatawa da Gobirawa Hausawa ne ba zai daddagu ba sai an kalli abubuwa da dama; da suka haɗa da labarin ƙasa da mazauna wuraren kafin da bayan jihadin ɗanfodiyo da al’adu da tadoji da kare-karen harsunan yankunan da wasu da dama.

Kamar yadda Bichiia Maisango ka bayyana ne, mutane ake magana, haka kuma kamar yadda Rabiu ka yi nuni tattaruwa waje ɗaya ke samar da ƙabila, haka ne, amma akwai abubuwa da ke shaƙure da zaman tare da ke canza lamurran al’umma suna so, ko ba su so.

Mu soma da batun birnin Sakkwato. Sararin da aka samar da birnin Sakkwato a yau tun kafin jihadi a cikin ƙasar Gobir yake, wannan ba tantama, wadda ita kuma take cikin nahiyar da ake wa laƙabi da ƙasashen/daulolin Hausa, a lokacin. A zagaye da wannan sarari inda Muhammadu Bello ya tanadar wa ɗanfodiyo domin zama da rayuwa a, wato inda Sakkwato take yanzu, akwai garuruwa da ƙauyuka mazauna wurin na asali, wasu Gobirawa ne, wasu Zabarmawa ne, wasu Buzaye ne, (farare da baƙake) wasu Fulani ne, (na gida da na daji) da wasu da dama.

Jaddada addini da karɓe mulki da Fulani suka yi a ƙarƙashin jagorancin ɗanfodiyo da mutanensa shi ya haifar da kafa da bunƙasar birnin Sakkwato a matsayin babban birnin Daular Usmaniyya baki ɗaya, a maimakon mazaunin da can na birnin Alkalawa, da aka samar tun a 1757, wanda shi ne babban birnin ƙasar Gobir da aka rushe da maye gurbinta a matsayin ganimar yaƙi. Wannan ya sa ƙasar Gobir ta koma ƙarƙashin mulkin sabuwar Daular Sakkwato, tun daga shekarar 1808. Wannan ne ya sa yankin ya tashi daga Gobir ya koma Sakkwato, al’ummar da ke cikin daular suka koma Sakkwatawa, maimakon Gobirawa. Hakan ya faru ne saboda Fulani da suka amshe mulki ba Gobirawa ba ne, a asali, dole su bambanta da waɗanda suka karɓe wa mulki. Shi ya sa ko sunan ‘jihadin’ da daular da aka kafa bayan nan aka dinga taƙaddama kan su, shin Daular Fulani ce ko Daular Sakkwato ko Daular Musulunci ce.

Wannan shi ya taimaka aka samar da al’umma mabambanta da suke zaune a wannan birni da kewayensa, da ma can nesa da shi, kuma ya haifar da karin harshen Sakkwatanci daban da Gobirci, wanda shi ne gadajje a yawancin faɗin yankin kafin jihadi, wanda ya ƙara tabbatar da cewa shi ne karin harshen ƙasar Gobir na asali ba Sakkwatanci ba. Ke nan Gobirci daban, Sakkwatanci daban.

Saboda haka idan aka yi nazari sosai za a iya fahimtar cewa akwai kamanci da bambancin tsakanin Sakkwatawa da Gobirawa da kuma Sakkwatanci da Gobirci ta fuskoki da dama. Wannan shi ya sa idan ana maganar Hausawa Zalla a wannan yanayi tsakanin Sakkwatawa da Gobirawa sai an buɗe littattafai da kundayen nazarce-nazarce da dama.

Wannan kuma wani darasi ne na daban, In sha Allah!

Farfesa Malumfashi, wanda malamin jami’a ne a Jami’ar Jihar Kaduna, ya wallafa ne a shafinsa na Facebook

By ukarofi