Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu
Sakamakon ci gaba da barazanar kai sabbin hare-hare a wasu sassan jihar Yobe, ranar Talata rundunar ‘yan sanda a jihar sun ɗauki matakin kulle kasuwar sayar da barasa, wadda aka fi sani da Mammy Market a babban birnin jihar dake Damaturu, matakin da ke da nasaba da kaucewa salwantar da rayuka dangane da shirin da mayaqan Boko Haram/ISWAP ke yi na kai sabbin farmaki.
Wannan wurin sayar da giya ta ‘yan sanda kuma ita ce kasuwar barasa mafi girma a birnin, wuri ne wanda ake ginin zai iya tsole idon mayaƙan bisa ga yadda kai sabbin hare-hare a takwarorinta zai iya shafarta, wanda a ‘yan kwanakin nan wasu mahara sun kai mabambantan farmaki a yankin Arewa maso Gabas kana da wasu a jihar Yobe, ciki akwai harin da Boko Haram suka kai wani gidan karuwai dake garin Gaidam inda suka yanka sama da mutum 10 tare da tayar da bam a gidan sayar da giya a Gashuwa, inda mutum ɗaya ya mutu bakwai suka samu raunuka.
Kasuwar wadda take cikin ‘Police Area Command Damaturu’, wanda hakan ya jawo hankalin rundunar ‘yan sandan yanke shawarar kulle kasuwar tsoron gudun abin da kan iya zuwa ya dawo, wanda hakan zai iya jawo maharan kitsa kai farmakin da zai ga zubar da jinin jama’a.
Bugu da ƙari, ranar Larabar da ta gabata, Boko Haram sun bayyana ɗaukar nauyin kai farmaki a gidan sayar da giya da ke garin Gaidam, mai tazarar kimanin kilomita 200 Arewa daga Damaturu babban birnin tare da na baya bayan nan, a Gashuwa, wanda ya jawo rasa rayuka da raunuka.
Wanda sakamakon matakin kulle Mammy Market ɗin, yayin da hakan ya shafi sauran wuraren sayar da giya da ke Damaturu, musamman a Unguwar Jerusalem tare da wasu shagunan da ake sayar da barasa.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa kasuwar sayar da barasar za ta ci gaba da kasancewa garƙame a lokutan shagulgulan Sallah, zuwa lokacin da tsaron ya ingaanta, domin kauce wa salwantar rayuka da dukiyar al’umma.
Da yake bayyana ɗaukar matakin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkareem, ya bayyana cewa, “rundunar ‘yan sanda ta ɗauki wannan matakin ne don kaucewa duk wata matsala tare da daƙile kutsen yan ta’adda.
“Saboda abubuwan da suka fari Gaidam da Gashua, sun ankarar damu wajen yin kan-da-garki tare da kulle wuraren sayar da barasa da ke cikin ‘Area Command Mammy Market’ har sai abin da hali ya yi. Sannan kuma ‘yan- sanda haɗi da sauran jami’an tsaro za su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen samar da ingantaccen tsaro don kare jama’a da dukiyoyin su,” ta bakin Dungus.
A nashi ɓangaren, mai bai wa Gwamnan jihar Yobe shawara kan harkokin tsaro, Dahiru Abdulsalam, burin mayaqan Boko Haram shi ne aikata abin da zai jawo hankalin jama’a da neman suna tare da sanya ƙyama tsakanin jama’a.
Haka zalika ya bayar da misali da farmakin bam ɗin da suka kai ya na daga cikin hanyoyin da suke amfani da su wajen neman goyon bayan al’ummar Musulmi da ke wannan jihar.
“Babban abin lura a dangane da abin da muka fi ɗauka da muhimmanci a sha’anin tsaron jihar Yobe shi ne kare rayukan jama’a a kowane ɓangare, a wuraren sayar da barasa ne, a gidajen sauke baqi, wuraren ibada da kasuwanni da makamantan su, wanda babban burinmu shi ne nemo sahihan hanyoyin da za mu daƙile kai waɗannan hare-hare,” in ji shi.
