Hukumar Kwastom ta buɗe iyakar Kamba a Jihar Kebbi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kwastom ta Ƙasa, NCS, a Litinin ta buɗe kan iyakar Kamba da ta haɗa Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar akan hanyar Kebbi a hukumance.

Gwamnatin Tarayya, ta wata sanarwa da hukumar NCS ta bayar a ranar Juma’a ta bada umarnin sake buɗe ofisoshin kan iyaka a Idiroko (Ogun); Jibiya (Katsina) Kamba (Kebbi) da kuma Ikom (Kuros Ribas).

Gwamnati ta rufe manyan kan iyakokin ƙasar ne a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile yaɗuwar annobar Korona da daƙile fasa-ƙauri domin bunƙasa noman shinkafa da sauran amfanin gona na cikin gida.

Yayin da ya ke jawabi wajen buɗe kan iyakar a hukumance a Kamba, shugaban hukumar kwastam na jihar Joseph Attah, ya bayyana fatansa cewa iyakar za ta buɗe wani sabon shafi na hulɗar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.

“Sake buɗe kan iyakar ba wai yana nufin an sake buɗe hanyar haramtaccen kasuwanci ba ne, a’a, an buɗe ne don amfanar juna ta fuskar tattalin arziki tsakanin ƙasashe biyu na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

“An sake buɗe kan iyaka don kasuwanci, da kuma inganta tattalin arzikinmu, amma ku lura cewa dokar hana shigo da shinkafa, kaji da sauran kayayyakin da aka hana shigowa da su har yanzu tana nan kuma rundunar da ke aikin sintiri za ta ci gaba da aiwatar da ita,” in ji shi.

By Editor