Tsauraran matakan gwamnatin Tinubu za su maida Nijeriya baya

Spread the love

Shekaru 64 da samun ‘yancin kai a Nijeriya, daga hannun Turawan Mulkin-mallaka na Birtaniya, har yanzu ɗan Nijeriya bai samu kyakkyawar kulawar da zai yi alfahari da mulkin Dimokraɗiyyaba, duk da wasu suna cewa ana Dimokraɗiyya a ƙasar, kuma tana aiki don talakawan ƙasa.

Abin da muke gani a yanzu na tsare-tsaren gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, wasu sabbin manufofi ne masu tsauri ga ‘yan Nijeriya, waɗanda ‘yan Nijeriya ba su yi zaton ganinsu a cikin gwamnatin Tinubun ba. Tun dai lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban Nijeriya, al’ummar ƙasa suka tsinci kansu a mawuyacin hali, a sakamakon ayyana janye tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi, wanda ta hanyar bada tallafin a ɓangaren mai ‘yan ƙasa na samun sauƙi. To sai dai tunda shugaba Tinubu ya cire tallafin a baki, aka shiga mawuyacin hali sakamakon ƙarin kuɗin litar mai daga N280 zuwa N650 a kowacce lita, wanda a yanzu kuma ya kai N998 a farashin gwamnati, yayin da gidajen man ‘yan kasuwa yake kaiwa N1150, ko N1200 duk lita.

Wannan al’amarin ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali, haka nan kuma ya ƙara yawaitar marasa aikin yi da ɓata-gari, domin da yawa daga cikin ma’aikatu da masana’antu haɗi da kamfanoni da dama sun rage yawan ma’aikata dalilin tsadar rayuwa, ƙarin harajin Vat da na wutar lantarki da sauransu. Wannan shi ya kai ‘yan Nijeriya suka fito zanga-zangar lumana a 1 ga watan August, sai dai kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba, haka zalika yanzu ma a ranar 1 ga Oktoba zanga-zangar da aka shirya yi bata yi tasiri ba, domin a jihar Kano tun kafin ranar 1 ga Oktoban, jami’an tsaro suka kama jagororin shirya zanga-zangar lumanar, duk kuwa da cewa sun fitar da sanarwar yin wannan zanga-zanga, da dalilin yinta, daga inda za su fara zuwa inda za su ke.

Idan muka yi la’akari da abin da ya faru a wannan zanga-zangar ta 1 ga Oktoban 2024, za mu fahimci cewa, duk yadda shugabanni suka kai ga takura talakawan ƙasa da azabtarwa gami da gasa musu gyaɗa a hannu babu damar su koka, domin gashi mun gani a zahiri. Tun kafin ranar jami’an tsaro suka riƙa yawo cike da motoci da makamai don barazana ga masu zanga-zanga, duk da cewa ‘yan ƙasa suna da dalilin kokawa dangane da abin da ake musu, amma a Nijeriya abin ba haka yake ba. Idan gwamnati ta zalunceka so take kayi mata godiya da nuna tana kan daidai, amma kai idan kayi kuskure sai an dangantaka da kotu an yi maka hukunci.

Duba da ire-iren waɗannan abubuwan da suke faruwa a yanzu, a kuma wannan gwamnatin mai ci ta Bola Tinubu, za mu iya cewa wani sabon mulkin-kama-karya ne ya dawo a Nijeriya. Idan har da gaske gwamnatin Tinubu gyara take so tayi ba zaluntar ‘yan ƙasa ba, mene ne dalilin ɗaukar waɗannan tsauraran matakan? Ya kamata a ce ba irin waɗannan matakan ya dace Tinubu ya ɗauka ba, muddin dai da gaske yake yi mulkin Dimokraɗiyya yazo yi ba kama-karya ba, domin wannan salon mulkin salo ne maras ma’ana, salo ne wanda zai fitar da al’ummar talakawan Nijeriya daga hayyacinsu (musamman al’ummar Arewa).

Tun kafin wannan lokacin da rayuwa tayi matuƙar tsada, a kan samu mutanen da suke shiga kowanne irin aiki don su ci abinci, a wancan lokacin ma kuɗin buhun shinkafa bai kai Naira dubu 30 ba, man fetur bai wuce 180 ba, abubuwa da dama basu yi tashin gwauron zabi ba, to ina ga yanzu da buhun shinkafa ya kai Naira dubu 72,000? Ko shakka babu, ina mai tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, na rantse da Allah waɗannan manufofin na gwamnatin Tinubu yana ƙirƙirarsu ne kawai don ya ƙara rusa Arewacin Nijeriya, kuma duk wanda yake musu yaje ya bincika ya gani. Ya koma shekaru 30 baya ya binciki tarihin Tinubu. Duk maganar da yake na cewa, “Ba neman kuɗi ya zo yi a mulkin Nijeriya ba” wallahi ƙarya ce da yaudara.

A wasu lokutan idan kana irin wannan maganar sai wasu su ce kasa ƙabilanci, babu maganar ƙabilanci a nan, abu ne a zahiri ba a baɗini ba, kuma tun kafin aje ko ina gashi mun fara gani.

Idan kana so ka tabbatar da abin da nake faɗa, to ka ziyarci kotuna daban-daban a nan Arewacin Nijeriya, ka saurari shari’o’in da ake yi a cikinsu, ka ziyarci ofisoshin hukumar Hisba, ko ofishin Ciɓil Defence na ko’ina a inda ka ke don gani tare da jin abubuwan da suke wakana. Zaka ci karo da kyasa-kyasai kala daban-daban, wanda mafi akasarinsu na da alaƙa da wannan uƙubar rayuwar da aka jefa mutane a ciki. Na ziyarci wasu wuraren da ake noma, akwai abubuwan al’ajabin da na gani da zai sa mutum zubar da hawaye, wani tunda yake ba a taɓa samunsa da rashin gaskiya ba, amma saboda yunwa da rashin abin hannu tasa yaje ya ɗebi masara a gona don ya kawo gida su ci tare da iyalansa.

Magana ta gaskiya ita ce, da Bola Tinubu yana son ‘yan Nijeriya suyi rayuwar farin ciki ne (musamman ‘yan Arewa da suka fi kowa shan uƙubar rayuwa), to da lokacin da aka rantsar dashi sai yayi kalar abin da Marigayi tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Alh. Umar Musa ‘Yar’adua yayi, wato rage farashin man fetur.

Ina mai tabbatar wa da al’ummar Nijeriya cewa, waɗannan matakan da Tinubu da gwamnatinsa ke ɗauka, za su ƙara taɓarɓarar da ƙasarmu ne, yunwa zata ƙaru, ƙuncin rayuwa zai ci gaba da yawaita, wannan kuma shi ne zai sa ayyukan ta’addanci su ci gaba da ƙaruwa. Haka nan satar kuɗin gwamnati ko in ce kuɗin ƙasa na al’umma zai ƙaru a wajen ɓarayin gwamnati. Buƙatun al’umma na ƙaruwa, yayin da kuɗin da suke samu basa iya biya musu rabin buƙatar da suke da ita, to wannan shi ne mabuɗin da zai bada damar satar kuɗin ƙasa, kullum ‘yan kasuwa su riƙa ƙara farashin kaya, rayuwa taci gaba da yi wa al’umma ƙunci. To da faruwar haka me ku ke tsaanin zai faru? Shin, tsanani ne ya ke sa mutane su dawo na kirki daga mutanen banza, ko kuwa kyautatawa ce take sauya mutane daga aikata ba daidai ba su dawo aikata abu mai kyau? Ya kamata kowa ya yi tunani a kan wannan.

A duk lokacin da tsanani ya tsananta, to mutane za su nema wa kansu mafita ne, kuma duk wani mai neman mafita ba ya jiran sai an ba shi umarnin yadda zai yi. Don haka, ku jagororin al’umma yana da kyau kuyi tunani, yana da kyau ku zamo ‘yan kishin ƙasa da al’umma na gaske ba wai ‘yan kishin ƙasa a maganganu irin na siyasa, ko na bugawa a jaridu da mujallu ba.

Mutane Nijeriya suna cikin matsin rayuwa, kuma ku shugabanni ku ne silar lalacewar komai, domin daga na gaba ake gane zurfin ruwa. Idan ku ka zamo adalai, shugabannin ƙwarai masu gaskiya da amana, tare da sauke nauyin al’umma da ke kanku a dalilin jagorantarsu da ku ke yi, to na tabbatar al’umma za su zamo na ƙwarai.

Batu na ‘yanci kuwa, zancen gaskiya a yanzu ɗan Nijeriya ba shi da wani ‘yanci, domin ‘yanci na nufin ka rayu cikin aminci a duk inda ka ke, ka samu ilimi, tsaro, magani a asibiti, hanya mai kyau, wutar lantarki, ruwan sha, ka faɗi albarkacin bakinka, kuma idan gwamnati ta ce za ta yi duk wani abu da ku ‘yan ƙasa bai muku ba, har ku ka fito ku ka ce ba kwa so, to dole gwamnati ta jingine wannan abun. Wannan shi ne ‘yanci, kuma ita ce (Democrate) wato dimokraɗiyya. Dimokraɗiyya ba kama-karya ba ce, tsarin mulki me mai cike da ‘yanci na ƙashin kai. Amma a nan Nijeriya ba haka abin yake ba, muddin kana son ka zauna lafiya a matsayinka na ɗan ƙasa, to sai dai duk abin da gwamnati ta ce zata yi ka zuba mata ido, koda abin yayi maka daɗi ko bai maka ba, koda ta dalilin shi za ka shiga cikin uƙuba, koda za ka rayu ko ka mutu. Kamar dai yadda muke gani a yanzu a wannan gwamnatin ta Tinubu, kuma an yi shiru kowa ya zama ɗan kallo.

Daga NAFI’U SALISU.

Marubuci/manazarci, daga Kano, Nigeria. [email protected]@gmail.com. 09056507471, 08038981211. 

By ukarofi