Ko za a dawo da yaƙi da rashin ɗa’a a Nijeriya?

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gwamnatin Tarayya ta ƙarƙashin Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA), ta fara gudanar da wani gangamin wayar da kan ’yan ƙasa game da muhimmancin girmama muhimman alamomin ƙasa, da a ko ina suke nuna ’yanci da ɗaukakar sunan Nijeriya. Waɗannan muhimman abubuwa da ake magana a kansu sun haɗa da tutar ƙasa, taken ƙasa, da takardun kuɗi na ƙasa. A ko ina aka ga waɗannan alamomi to, tabbas abin da suke alamantawa shi ne ƙasarmu, kuma ƙasar iyaye da kakaninmu.

Idan wasu daga cikin mu za mu iya tunawa, lokacin gwamnatin mulkin soja ta tsohon shugaban Nijeriya Janar Muhammadu Buhari da wacce ta biyo baya ta tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida, akwai wasu shirye-shirye da gwamnati ta ɓullo da su da suka haɗa da shirin Yaƙi da Rashin ɗa’a na WAI, wanda a Turance ake kira da War Against Indispline, da kuma shirin Kyautata Halayyar ‘Yan ƙasa na MAMSER. Dukka waɗannan tsare-tsare ne da aka ƙirƙiro su domin kyautata halayyar ’yan Nijeriya wajen nuna halin ya kamata, kishin ƙasa, da sadaukarwa, domin tsare martabar Nijeriya a idon duniya. Sauran gwamnatoci ma duk sun ɓullo da irin nasu shirye-shiryen, da nufin kyautata halayyar ’yan ƙasa, irin su ‘Sauyi Daga Kaina Ya Fara’ wato Change Begins With Me!

Abin takaici ne sosai yadda sunan Nijeriya da ’yan Nijeriya yake lalacewa a ƙasashen waje, sakamakon irin halayyar da muke nunawa, a ƙasashen da muka je a matsayin ’yan ci rani, neman ilimi, ko kasuwanci, amma sai a riƙa kama wasu ’yan uwan mu, bisa zargin aikata ayyukan da basu kamata ba, suna damfarar jama’a, suna karya doka, suna shiga ƙungiyoyin asiri da na ’yan ta’adda suna aikata ɓarna, da kuma safarar makamai, safarar miyagun ƙwayoyi ko safarar mata da ƙananan yara, suna zuwa ƙasashen turawa da Larabawa suna aikata karuwanci da ayyukan wahala. Lalacewar har ta kai ga idan ɗan Nijeriya ya sauka a filin jirgin saman wata ƙasa, sai an riƙa masa wasu tambayoyi na daban, ana yi masa binciken ƙwaƙwaf, don kar ya shiga cikin ƙasar ya haifar musu da wata matsala ko ya cutar da ’yan ƙasar su.

Sakamakon wani bincike da cibiyar nazarin ayyukan laifi na ƙasa da ƙasa ta duniya ta Global Initiatiɓe Against Transnational Organized Crime, ta gudanar ta gano cewa, Nijeriya ce ƙasa ta 6 a duniya, dake da yawan masu aikata laifuka, wacce adadin ƙiyasin da aka yi har ya kai 7.28. Kodayake a cikin wani rahoto da Babban Sufeton ‘Yan sanda na ƙasa Kayode Egbetokun ya fitar cikin wata Yuli da ya gabata, ya bayyana cewa, an samu raguwar aikata laifuka a ƙasar nan, amma shin hakan ya canza yadda ake kallon mu a ƙasashen waje.

Sai dai ko a wannan makon mai ƙarewa, ’yan wasan ƙwallon ƙafa na Super Eagles da ke wakiltar Nijeriya a gasar cin kofin ƙasashen Afirka sun fuskanci cin zarafi, a ƙasar Libiya, inda aka tsare su a filin jirgin saman ƙasar ba tare da wani bayani ba, har na tsawon awoyi 16. Wannan abin ya janyo aka soke wasan, saboda ƙorafin da maihorar da ’yan wasan ya yi, inda ya nuna ɓacin ransa ga abin da ya faru. Kuma ya ce, ’yan wasan ba za su sadaukar da rayuwarsu a wannan yanayin da ake ciki na rashin ingantaccen tsaro a Libiya, su kama hanyar zuwa Benghazi ba.

La’akari da irin waɗannan abubuwa na tsangwama da kyara da ’yan Nijeriya suke fuskanta a wasu ƙasashen, saboda zargin da ake yi musu, da kuma yadda mu kanmu ‘yan Nijeriya a cikin ƙasa muke raina darajar ƙasarmu da shugabanninta, ya sa Hukumar NOA ta ɓullo da wannan tsari, wanda ya ƙunshi shirye-shirye daban-daban a ciki. Batun girmama alamomin ƙasa, rera taken ƙasa da girmama shi, da kuma ƙaddamar da shirin National Identity Project, wanda zai mayar da hankali kan ƙara dasawa ’yan Nijeriya kishin ƙasa, ƙarƙashin taken, ‘Ni ɗan Nijeriya Ne Na ƙwarai’, wato I Am A Real Nigerian. Waɗannan tsare-tsaren a cewar jami’an Hukumar NOA an ɓullo da su ne, bisa la’akari da yadda kishin ƙasa ke zaizayewa a zukatan matasa.

Abin takaici ne ka ji ɗan Nijeriya saboda yunwa ko talauci ya riƙa aibata sunan ƙasar sa yana kiranta da Nijeriya Jaga-Jaga, ko ma ya murguɗa sunan zuwa Lanjeriya. Wasu ma kullum burinsu su gudu su bar ƙasar saboda tunanin babu wani abin alheri da zai faru da ƙasar, wai kullum baya take komawa. Ko kuma ka ji wasu na kiran cewa, dama a yi juyin mulki sojoji su karɓe ragamar jagorancin ƙasar da hannun zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula.

Waɗannan abubuwa ne marasa daɗi da bai kamata a samu wani ɗan Nijeriya yana furta su ko aikata su ba. Saboda yadda yake nuna tsantsar rashin kishin ƙasa da rashin sanin ciwon kai. Ganin dacewar wannan gangami na Gwamnatin Tarayya ya sa ni yin wannan rubutu, ba don matsalolin da ƙasar ke fuskanta ba sa damu na ba. Ba kuma don rashin shugabanci nagari da karyewar tattalin arziƙin ƙasa bai dame ni ba ne. Lallai na damu ƙwarai, kuma ina cikin talakawan ƙasar nan da sauyin rayuwa yake jijjiga su. Amma hakan ba zai sa in aibata shugabanni ko kushe ƙasata ba!

Sharhin da muke yi kowanne mako a wannan kafa, da shawarwarin da muke bayarwa ga gwamnati da sauran ’yan ƙasa, na daga cikin irin gudunmawar da muke bayarwa, don ganin an samu sauyi a halayyar ’yan Nijeriya. Babu shakka akwai buƙatar a sake waiwayar tsarin yaƙi da rashin ɗa’a da kyautata halayyar ’yan ƙasa, domin ɗora matasa da sauran yara masu tasowa kan turbar kishin ƙasa, da dasa musu son ƙasa da alfahari da ita a matsayin ƙasar iyayenmu abin alfaharinmu.

Sanin mutuncin kanmu ne da martabar ƙasarmu, mu tabbatar da ganin ba mu ɓata muhallinmu da dukiyar gwamnati ba, da nuna halin ko in kula da ayyukan da gwamnati ta samar don jin daɗin jama’a. Ba za mu yarda a yi amfani da mu wajen karɓar cin hanci da rashawa ba, ko yunƙurin bayarwa don hana doka aikinta, ko cin amanar dukiyar ƙasa a yayin da aka amince mana aka ba mu amanar ƙasa ko wani muaami. Kada mu yarda a haɗa baki da mu a sayar da mutuncin ƙasar mu, ko tada zaune tsaye, ko tarzoma, don cimma burin wasu. A duk lokacin da aka ambaci sunan Nijeriya a ga muna nuna alfahari da jin shauƙi, in ana rera taken ƙasa a ga natsuwa a tare da mu, kuma mu riƙa karanta kalmomin cikin sanin ma’anoninsu da kishin ƙasa a cikin ranmu.

Ba zai yiwu mu yar da tutar Nijeriya a ƙasa ba, ko mu taka ta da ƙafafunmu da nufin wulaƙantarwa, ko ƙonawa da wuta, ko sauke ta da ɗaukaka tutar wata ƙasa a cikin ƙasarmu ba. A cikin gidajen mu da ofisoshinmu a ga mun maƙala tutar Nijeriya da kiyayewa, haka ma a cikin abubuwan hawan mu, a ga tutar Nijeriya tana kaɗawa.

Wani abu ya taɓa faruwa wata shekara a ƙasar Ghana, yayin wata gasar ƙwallon ƙafa da aka buga tsakanin ƙasar da Nijeriya, wanda Allah ya bai wa ’yan wasan Nijeriya nasara. Sai dai abin da ya faru a lokacin ya zama darasi ga ’yan Nijeriya na lokacin har zuwa yanzu. Domin kuwa ’yan Nijeriya mazauna ƙasar Ghana sun nuna farin cikinsu sosai da wannan nasara da ’yan wasan ƙasar su ta gado suka samu akan na ’yan ƙasar da suke zaune. Don haka sun fita titunan Babban Birnin ƙasar cikin motoci suna murna tare da ɗaga tutar Nijeriya sama, yayin da wasu kuma suka saukar da tutar ƙasar Ghana suna jan ta a ƙasa. Wannan abu ya yi matuaar ɗaga hankalin ’yan ƙasar Ghana, har ma da waɗanda asalin iyaye da kakaninsu tushen su daga Nijeriya ne. Sakamakon wannan abu rikici ya ɓarke tsakanin ’yan Nijeriya da ‘yan Ghana, abin da ya haifar da lalacewar dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu, har na tsawon wani lokaci.

Abin da wannan ke nuna mana shi ne ba zai taɓa yiwuwa wata ƙasa ta lamunci ganin an wulaƙanta mata tuta ba, wanda hakan ke nufin ita ƙasar kai-tsaye aka wulaƙanta. To, me zai sa mu a matsayin mu na ’yan Nijeriya da muka san ciwon kanmu za mu riƙa wulaƙanta tamu tutar da raina duk wata alama da ke nuna kima da martabar ƙasarmu.

Mu daina raina kuɗin ƙasarmu, na Naira, duk kuwa da karyewar darajarsa a halin yanzu, har muna fifita amfani da Dalar Amurka ko Euro, don ganin darajarsu ta fi ta kuɗin mu. Ya kamata mu fifita ciniki da kuɗin ƙasar mu, mu daina watsi da shi muna takawa a wajen biki, ko yin rubuce-rubuce na shirme a kai, alhalin hakan bai kamata ba.

By ukarofi