Tsohon ɗan wasan bayan Manchester United, Real Madrid da Faransa, Raphael Varane, ya yi ritaya daga buga ƙwallo yana da shekara 31.
Varane ya koma Ƙungiyar Como ta Italiya kyauta a watan Yuli amma ya ji rauni a gwiwarsa a wasansa na farko da Sampdoria a watan jiya.
Ɗan wasan bayan ya ce zai ci gaba da zama a ƙungiyar amma ba zai taka leda ba.
Varane ya fara taka leda a Lens ta Faransa amma ya shafe kakar wasa ɗaya a ƙungiyar ta farko kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2011.
Ya ji daɗin zama na tsawon shekaru 10 a babban birnin Spain, inda ya lashe kofuna 18 – ciki har da kofunan La Liga uku da na gasar zakarun turai huɗu.
Mai tsaron bayan ya koma Old Trafford a lokacin hada-hadar ‘yan wasa na 2021 kan fam miliyan 34 na farko, inda ya buga wasanni 95 a duk gasa.
Ya lashe kofin Carabao a shekarar 2022 kuma wasansa na ƙarshe a ƙungiyar shi ne nasarar cin kofin FA na ƙarshe a kan abokan hamayyarta Manchester City a Wembley a watan Mayu.
Varane ya buga wasansa na farko a Faransa a shekara ta 2013 kuma ya buga wasanni 93, inda ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, da gasar Nations League a shekarar 2021 kuma ya sake kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.
