
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta yi wa tawagar ministocinsa garambawul.
Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya bayyana hakan wa wakilan Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda ya ce gwamnati ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na farfaɗo da tattalin arziƙi wanda al’umma ba ta sani ba.
Onanuga, ya ce Shugaba Tinubu ya umarci ministocinsa su ke bayyana wa al’umma ayyukan da ma’aikatu da dama ke yi na inganta ƙasa.
A baya ne Tinubu ya sha alwashin yin nazari game da ayyukan ministocin wanda hakan ne zai sanya shi yin hukunci game garambawul ɗin da ya ƙudiri aniyar yi.
Akwai matsawa daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta APC kan rashin ƙoƙarin wasu ministocinsa na kan cewa a sallami ire-irensu.
Watanni goma kenan da Tinubu ya yi gargaɗin yin garambawul ɗin wanda har zuwa yanzu bai sauya kowanne su ba in ban da dakatar da Ministar Ma’aikatar Jin-ƙai, Dakta Betta Edu da ya yi.
