Shettima ya nemi a samar da mafita ta dindindin ga yaƙin Gaza

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin duniya su samar da mafita ta dindindin game da yaƙin Gaza da ake cigaba da yi.

Ya ce, akwai buƙatar al’ummar Palestine su samu ƴanci ganin yadda ake cigaba da ɗaiɗaita su.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin yayin muhawara da shugabannin duniya a taron game da batutuwan da suka shafi al’umma.

A ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 ne aka fara yaƙin Gaza a ƙasar Palestine wanda ya haifar da ɓarna da dama inda aka rasa rayuka 1,143 da dubunnan mutane da suka samu raunuka.

Yankin Gaza shi ne inda aka fi rugugin wuta a tsakanin sojojin Isra’ila da na Palestine wanda hakan ke cigaba ɗaiɗaita al’umma tare da jikkata su.

Shettima ya yi kira ga shugabannin duniya da su samar da mafita ta dindindin ga yaƙin Isra’ila da Palestine inda ya ce rashin yin hakan nuna gazawa ce daga cimma manufofin majalisar.

By Babaji