
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya kai ƙarar Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ga Kotun Ƙoli kan shelanta shi a matsayin wanda ake nema.
EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello ne da hannu a laifuka 19 bayan zargin sa da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 80.2.
A ranar Laraba ne aka buƙaci Bello ya halarci babban kotun tarayya don sauron ƙarar da ke kansa.
Saidai, a lokacin fara tattaunawa kan batun, tawagar lauyoyin da ke kare Bello ƙarƙashin jagorancin A. M. Adoyi sun shaida wa Alƙalin da ke kan shari’ar, Mai Shari’a Emeka Nwite kan cewa akwai batun ɗaukaka ƙara na cewa sun shigar da takardar tun a ranar 23 ga watan Satumba.
Takardar ta na ɗauke ne da batun dakatar da takardar kamu da aka fitar akan Yahaya Bello tun ranar 17 ga watan Afrilu.
Adoyi ya nemi kotun ta dakatar da batun tsarewar zuwa lokacin da sakamakon Kotun Ƙoli zai fito.
Kawo yanzu an ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba don yanke hukunci.
