Tsohon ministan tsaron Ukraniya ya nemi a yi zaɓen shugaban ƙasa duk da yaƙinsu da Rasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Tsaron ƙasar Ukraniya, Mykhailo Fedorov ya yi kira da a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa duk da yaƙin da ke tsakanin ƙasar da Rasha, a wani yanayi da za a kira da ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa da Shugaba Volodymyr Zelenskyy zai iya fuskanta tun bayan fara yaƙin a 2022.

Fedorov mai shekaru 35, ya yi wannan kira ne a wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce wajibi ne ƙasar ta dawo da tsarinta na dimukraɗiyya duk da cewa ana cigaba da gwabza yaƙi tsakaninta da Rasha.

Saidai, duk da cewa tsohon ministan bai ambaci Zelenskyy ba yayin jawabin nasa, ana ganin kalamansa kai tsaye suna ƙalubalantar matakin shugaban ne game da zaɓuka a lokacin yaƙin.

Ƙasar a halin yanzu tana ƙarƙashin dokokin sojoji kuma an haramta zaɓuka a ƙarƙashin dokar Ukraniya yayin da na sojoji ke aiki. A baya ne Zelenskyy ya ce za a iya yin zaɓe matuƙar an samu halin tsaron rayukan al’umma.

A watan Yuli ne aka tsige Fedorov a matsayin ministan tsaron ƙasar bayan wata shida a kan muƙamin. Wannan mataki ya janyo fargaba a jagorancin sojin ƙasar da zanga-zanga a Kyiv da wasu birane, inda jama’a suka riƙa kiran a dawo da shi kan matsayin.

Hakan ya biyo bayan kyakkyawan shaida da aka masa ne na aiki a sauyin da Ukraniya ta samu a fannin dinital da kuma gudumawar da ya bayar wajen zamanantar da harkokin tsaron ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply