Daga WAKILINMU
Tsohuwar matar Sarkin Dutse, Hajiya Asiya Nuhu Sanusi, ta maka Sarkin Dutse, Ahaji Hamim Nuhu Sanusi, a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a kan abin da ya shafi gado.
Asiya tare da wasu mutum bakwai sun maka Sarki Hamim Nuhu Sanusi da wasu mutum shida a kotu ne inda suke ƙalubalantar hukuncin da Kotun Upper Shari’a 1, ƙarƙashin jagorancin Khadi Ado Birnin Kudu ta yanke kan batun gadonsu.
Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, ƙarar wadda suka shigar ta hannun Barista Abdulhali Ali Esq, ta haɗa da Kotun Upper Shari’a 1 inda a nan aka fara shigar da batun.
Cikin ƙarar mai lamba SCAJG/CV/2023, matar tsohon sarkin ta buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a da ta tantance ko kotun farko ba ta yi kuskure ba wajen ƙwace kadara mai lamba 17 JGNL/DU/RES/94/264 wadda maigidanta ya ba ta kyauta a lokacin da yake raye, tare da maida kadarar cikin kayan gado.
Haka nan ta buƙaci Kotun da ta tantance ko wasiƙar da marigayin ya miƙa mata game da kadarar a halin rayuwarsa wadda ta gabatar wa kotun ba ta isa shaida ba.

Ƙarar ta nuna cewa kafin rasuwarsa, marigayin ya bai wa kowacce daga matansa gidaje bibbiyu, amma sai Kotun farko ta karɓe gidajen Asiya sannan ta amince da na sauran matan.
Majiyarmu ta ce ya zuwa haɗa wannan labari Kotun ba ta tsayar da ranar da za ta saurari wannan ƙarar ba.
Kuma ƙoƙarin da ta yi don ta bakin kakakin Masarautar Dutse ya ci tura.