Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Tun janye tallafin man fetur da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a jawabin sa karɓar mulki ranar 29 ga watan Mayu a ka shiga ganin sauye-sauye ta fuskar tattalin arziki da kusan dukkan lamuran da su ka shafi rayuwar yau da kullum.
Masu sharhi ma sun yi ta bayanin ainihin abun da ya faru na tashin farashin nan take tun gabanin aƙalla watan jiya na Yuni da a ka yi bayanin sai watan ya kare ne tallafin da a ka ciren zai kammala wato a wannan watan a Yuli sai a buɗe sabon babi na rayuwa ba tallafi. Duk lamuran ƙasa a kai tsaye ko a kaikaice su na da alaƙa da man fetur da hakan kan sa da zara wani abu ya shafi man fetur musamman in ƙarin farashi ne kamar yadda ya saba faruwa sai a gyara sauran sassan ma su tashi.
Tun tsohon shugaba Buhari ya na kamfen ya ke nuna sam bai ga amfanin batun tallafin ba don tamkar ya na amfanar wasu mutane ne ƙalilan ko ’yan jari hujja amma duk da haka har ya sauka daga mulki a tsawon shekaru 8 bai kawar da tallafin ba sai dai ya saita cire tallafin ya bar wa magajin sa Tinubu ya zo ya cire.
A yau wa imma tallafin ’yan jari hujja ya ke amfana ko talakawa ma na amfana da tsarin to an riga an gane. Dama a irin waɗannan ƙasashen masu tasowa sai masu hannu da shuni sun koshi sun shure ne talakawa kan lasa. Da zarar an toshe hanyar da ’yan baranda ke samun na garabasa sai su ɓullo da hanyoyin fitar da ribar su daga jikin talakawa!
Yanzu dai talakawa ke biyan kuɗin tallafin a madadin abun da gwamnati ke yi a baya. Don haka ba a rabu da Bukar ba wai an haifi Habu. Biyan tallafin da talakawa ke yi don a kawo fetur ya fi ma na gwamnatin tsada in ka deve bayanan da a ke cewa akwai cin hanci da rashawa ko zamba cikin aminci a gaskiyar fetur ɗin tallafi da a ka shigo da shi a baya.
Ma’ana wasu na cewa za a iya shigo da lita misali 5 a yi lissafin ta a kan 10 ne koma 20. Ko ma dai yaya ai jami’an tsaron sirri da shi kan sa kamfanin fetur NNPCL sun san gaskiyar yadda lamuran ke faruwa don haka mu dai na mu amfani da zahiri ne in ma mun yi ɗan shiga bayaiyun bayanai sai waɗanda za mu iya nuna shaida a kai gama ƙasar nan ba a karambanin bayyana abun da mutum ba shi da shaida mai kwari kar ya gamiu da fushin masu fushi da fushin wani.
Hatta shawarin da wasu ke bayarwa na a gyara matatun mai ba ya samun karɓuwa don kuwa ba mamaki haka a ka tsara ƙasar ta kasance ko ma in ce hakan shi ne tubulin da ya riƙe Nijeriya. Kar a kasa fahimta ta a nan ina nufin masu amfana da yanayin za su kyale ƙasar ta dan sarara in su na amfana amma da zarar an toshe hanyar za su kuwa fito da wannan hanya mai tsauri. Yo ai mutum ba zai iya tare kogi ko hanyar ruwa ba in damuna ta yi kuwa za a ga amsa.
Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya ce tamkar kasuwa ke yin halinta a yanzu kan fsrashin litar fetur biyo bayan yadda litar ta zama ba tabbas don shiga hannun ’yan kasuwa da lamarin ya yi kacokan tun da gwamnati ta zare hannun ta.
Shugaban kamfanin Mele Kolo Kyari ya bayyana a yayin da litar fetur ta ƙara cillawa sama zuwa fiye da Naira 600. An wayi gari a ka fara gani daga gidajen man fetur na kamanin sun canja litar zuwa Naira 617.
NNPCL na cewa yadda dan kasuwa ya sayo kayan sa haka zai je kasuwa ya sayar don ya samu riba. Wannan kuwa a fili ya nuna sai yadda ’yan kasuwa su ka ga za su samu gagarumar riba sannan su sayar. Masu sayen mai ai ba su da katavus ko su saya ko su bari. A baya ai a kan iya ƙorafi cewa mai ya yi tsada a duba amma yanzu abun da a ke son a nuna shi ne kayan ’yan kasuwa ne ba hannun gwamnati ko da na sa baki ne a ci ƙaramar riba a lamarin.
Tuni mutane ke sharhin lalle in an bar ‘yan kasuwa na tsara farashi yadda ran su ke do; to ƙazamar riba za su rika nema don maye gurbin wa imma daidai ko ma fiye da yadda su ke samu lokacin da a ke ba da tallafi. Kuma daga yanzu kenan ba tsayeyyen farashi duk yadda dala ta yi sama ko kasa shikenan sai a juya inji a mayar yanda za a ci riba. Kacokan ’yan kasuwa sun karɓi akalar mai kenan ba wata hanya sai ta ajiye mota ko rage yawan zirga-zirga da hakan kuwa tabbas zai shafi kuɗin shiga ko ingancin rayuwar yau da kullum.
Bs shakka qarin farashin zai shafi farashin dukkan kayan masarufi fiye da abun da a ka gani a makon jiya. ’Yan kalilan ne a cikin ‘yan kasuwa za sui ya jiran sai sun sayar da tsohon kaya kafin fara aiki da sabon farashi a sabon kaya da ya ƙara kuɗi.
Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyoyin Arewa Nastura Ashir Sharif ya ce da alama burin ‘yan jari hujja su kai farashin litar mai Naira 1000.
Shariff wanda ke magana biyo bayan ƙarin tashin farashin fetur; ya ce muradin ‘yan barandan fetur samun tara dukiyar da ba za su iya kashewa ba a tsawon rayuwar su.
“Matukar aka bar ‘yan jari hujja da akalar farashin fetur zuwa Disamba sai sun kai lita Naira 1000”
A nan jagoran qungiyoyin ya buƙaci shugaba Tinubu ya shigo ya sanya baki a tsakanin ‘yan kasuwa da jama’ar ƙasa don kar tura ta kai bango.
Hakanan Sharif ya ce ba daidai ne a kwatanta farashin litar fetur da lamarin yadda wayar salula tun ta na tsada har ta yi araha ba don hanyar mota daban da ta jirgi. Irin wannan sharhi a kan same shi ga ma masana tattalin arziki da ke nuna in an bar kasuwa ta yi halin ta za a samu gasa tsakanin kamfanonin mai da a ƙarshe lalle farashin zai iya faɗowa.
A al’adun Nijeriya ba bisa dokokin ilimin tattalin arziki ba man fetur ba ya saukowa ko kuma a ce shi tsarin sa daban ne don kuwa ya na shafar rayuwar kowa a inda ɓangaren wayar salula bai zama wajibi sai kowa ya saya ko lalle sai kowa ya zuba kuɗi a wayar sa ya yi ta bugawa a dogayen lokuta ba.
Sharif ya yi ta yin tambayar wasu kayan masarufin ma da su ka ƙara kuɗi su ka ƙi saukowa kamar shinkafa yanzu kuma a na maganar masara ma ta cilla sai yadda hali ya yi.
Gwamnatin Tinubu ta ce za ta yi bitar shirin ta na rage raɗaɗi wajen tura Naira duba 8000 ga kowane daga gidajen talakawa miliyan 12 a faɗin ƙasa don rage ƙuncin cire tallafin mai.
Wannan dai mataki ne don yadda jama’ar ƙasa su ka soki shirin da nuna ba wani tasirin da zai yi.
Mai ba wa shugaban shawara kan sadarwa Dele Alake ya bayyana sake shawarar a wata sanarwa.
Yanzu dai an ba da umurnin sake tsarin nan take tun da jama’a sun bayyana ra’ayin da ya sha bamban da na gwamnati.
Alake ya ce, ai wannan tura kuɗin ma na cikin wasu tsare-tsare ne ko tsari ɗaya ne kaɗai cikin abubuwan da gwamnati ta ke da shirin yi wajen rage raɗaɗin.
Shugaba ya ce ba zai barazanar ƙarancin abinci ta nakkasa ‘yan Nijeriya a matakan alwashin kawar da abubuwan da ke barazana ga noma da samar da abinci.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar da rahoton hasashen samun ƙarancin abinci a Nijeriya musamman yankin arewa maso gabar inda a wasu dazuka ‘yan ta’adda ke yiwa manoma barazana ta hanyar kisan gilla ga wasu manoman.
Ba mamaki shi ya sa shugaban alwashin magance ƙalubalen da ya hada har da ambaliyar ruwa.
Abdulaziz Abdulaziz mai taimakawa shugaban kan labaru ya yi ƙarin haske da cewa “za a rabawa manoma taki da iri kuma za a faɗaɗa dazuka don noma kazalika an tsaurara matakan tsaro”
A nan babban manomi Isa Tafida Mafindi ya ce sai fa an ɗau matakan zahiri fiye da samar da iri ko taki don ba su kaɗai za su sa bunƙasar nom aba sai gwamnati ta kai ga share dazuka da samarda na’urori sannan manoma za su samu fa’idar tsarin.
Kammalawa;
Nijeriya mai kimanin mutum miliyan 200 na da akasarin jama’a da ke rayuwa a qasa da ma’aunin talauci na Majalisar Ɗinkin Duniya na samun ƙasa da dala daya a wuni wato wajajen Naira 750 a yanzu inda janye tallafin fetur ya ƙara zafafa ƙuncin amma duk da haka nasarar barin amfani da tsoffin kufi ya sanyaya zuciyar jama’a. Ya na da muhimmanci mutane su riƙa yin iya lamura na wajibi su daidaita rayuwar su daidai da yanda ƙalubalen nan ke ƙaruwa. Daidai ruwa daidai gari.