Tufka da warwara kan cire tallafin fetur

•Rahoton Majalisar Zartarwa ya ci karo da kalaman Shugaban Majalisar Dattawa

•Tallafin wata shidan farko mu ka saka a kasafin 2022 – Ministar Kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatoci da dama da suka shuɗe a Nijeriya sun ci alwashi da ɗauka wa talakawan ƙasar alƙawarin za su sayi man fetur cikin rahusa ta hanyar ware wasu maqudan kuɗaɗe, domin bayar da tallafi.   

Sai dai wasu alƙaluma da gwamnati ke fitarwa sun nuna cewa, a na kashe kusan Naira biliyan 250 duk wata a matsayin kuɗin tallafin, wanda gwamnati a yanzu ke cewa ya yi yawa, kuma ta na so ta yi amfani da su a wasu manyan ayyukan raya ƙasa.

Duk da cewa, wasu gwamnatoci a baya ba su yi nasara ba a yunƙurinsu na cire tallafin, Gwamnatin Shugaba Buhari ta ci alwashin cire shi biyo bayan kafa sabuwar dokar man fetur mai suna ‘Petroleum Industry Act’ (PIA), wacce ta mayar da kamfanin Kula da Harkokin Mai na Nijeriya (NNOC) na kasuwanci zalla, maimakon na gwamnati ita kaɗai.

Batun cire tallafin, a wannan makon ya mamaye kanun labarai a Nijeriya, sai dai har yanzu jama’a sun kasa gane matsayar da aka kai kan batun, duba da yadda ɓangarori na masu ruwa da tsaki akan lamarin ke tofa albarkacin bakinsu ta hanyar yin harshen damo.

Bayanai masu cin karo da juna sun fara ɓulla daga fadar gwamnati a baya-bayan nan kan cirewa ko barin tallafin, wanda farashinsa zai kai fiye da Naira 300, idan gwamnati ta yi nasarar cire shi ɗin.

Yayin da Ministar Kuɗi ta Nijeriya ke cewa, an saka ƙudirin a cikin kasafin kuɗi na 2022 ne na tsawon watanni shida kawai, shi kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, yana cewa, Shugaba Buhari ya faɗa masa cewa, bai umarci kowa da ya ya cire tallafin ba.

A watan Oktoban 2021, Ministar Kuɗi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana wa ‘yan ƙasa cewa, gwamnati ta shirya, domin mayar da harkar man fetur ta ’yan kasuwa zalla, tana mai cewa, kuɗin da za a biya tallafi na wata shida na farkon 2022 kawai suka saka a kasafin kuɗi.

“Cikin kasafinmu na 2022, mun saka kuɗin tallafi na wata shidan farko, sauran rabin kuma mu na yunƙurin sauya sashen zuwa na ’yan kasuwa, don mu riƙa adana kuɗaɗen ƙasar waje da kuma samun ƙarin riba daga fetur da iskar gas,” inji Zainab Ahmed.

Ta ƙara da cewa, gwamnati na sa ran nan da watan Yuni za ta daina biyan tallafi kwatakwata.

“Idan mu ka kalli tsabar kuɗi Naira biliyan 250 da ake kashwa duk wata, wanda kuma ya ke ta ƙaruwa, hakan na nufin kamfanin mai na NNPC zai samu ribar Naira biliyan 120 kenan. To, yanzu kuma mun fara shiga yanayin da NNPC ba ya iya samar da ribar ko ƙwandala.

“Idan ka tara Naira biliyan 250 sau 12, kusan Naira tiriliyan uku kenan. Idan ba mu cire wannan kuɗin ba, to abin da za mu ci gaba da biya kenan. Wannan kuɗi ne da za mu iya amfani da su a ɓangaren lafiya da ilimi.”

Ta ce, sabuwar Dokar Man Fetur ta PIA ta tanadi cewa, “wajibi ne gwamnati ta zare hannunta daga ƙayyade farashin mai.”

A ranar 31 ga Disamba, 2021, Shugaba Buhari ya sanya wa dokar kasafin kuɗin hannu bayan mako biyu da Majalisun Wakilai da ta Dattawa suka amince da shi bayan sun kammala nazari da gyare-gyare.

Kazalika, ministar ta ci gaba da cewa, za a yi amfani da kuɗin tallafin wajen raba wa ‘yan Nijeriya mafiya buƙata, ta hanyar ba su dubu biyar-biyar a matsayin alawus na sufuri, sannan za a biya kuɗin ne ta hanyar intanet kamar E-Naira da sauransu.

“Za mu zauna mu duba yawan mutanen, amma mun amince cewa za mu bai wa mutum miliyan 20 zuwa 40 ta hanyar tura musu ta intanet, mun fahimci cewa, tsarin kuɗin zamani na E-Naira zai taimaka da sauran hanyoyin biyan kuɗi,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa, za a tura wa mutane kuɗin ne tsawon wata shida zuwa 12. Sai dai ba ta bayyana takamaiman adadin kuɗin da za a raba wa ‘yan Nijeriyar ba, tana mai cewa suna ci gaba da tattaunawa.

Sai dai a ranar Litinin da ta gabata kuma, da ya ke magana da manema labarai a yammacin Talata bayan ganawa da Shugaba Buhari a Abuja, Sanata Ahmad Lawan, ya ce, Shugaban Ƙasar ya faɗa masa cewa, bai nemi wani mutum ya bi hanyoyin cire tallafin ba.

“Da yawanmu mun damu da fafutikar baya-bayan nan da zanga-zanga. Mutanen mazaɓarmu sun damu matuƙa cewa, gwamnati za ta cire tallafin man fetur. Saboda haka a matsayinmu na ‘yan majalisa abu ne mai muhimmanci,” a cewar Ahmad Lawan.

Sanatan ya qara da cewa: “Na ga cewa ya zama dole na ziyarci Shugaban Ƙasa a matsayinsa na jagora don tattauna abubuwan da suka damu ‘yan ƙasa, kuma ina mai farin cikin shaida muku cewa shugaban ƙasa ya faɗa min bai tava faɗa wa kowa ba cewa ya kamata a cire tallafin fetur.”

Amma kwana biyu bayan waɗancan kalamai na Shugaban Majalisar Dattawa, sai dai wani yanayi mai kama da tufka da warwara ya sake ɓulla, inda a gefe guda kuma ranar Laraba da ta gabata, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, wacce Shugaba Buhari ke jagoranta ministocinsa a cikinta, ta amince da shawarar da Kwamatin Musamman na Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, wanda ke ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya nemi a cire tallafin tare da ƙara farashin man fetur a Nijeriya.

Yayin da ake tsaka da wannan muhawarar, wani rahoto da jaridar intanet ta TheCable ta ruwaito a safiyar Laraba ya ce, Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, ‘National Economic Council’ (NEC) ta bai wa Gwamnatin Buhari shawarar ƙara farashin mai nan da watan Fabrairun wannan shekara.

Rahoton ya ce, majalisar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta nemi a mayar da lita ɗaya na fetur zuwa Naira 305. Majalisar ta dogara da rahoton kwamitin da Gwamna El-Rufai ke shugabanta ne wajen yanke wannan shawara, kamar yadda jaridar ta ruwaito, inda suke son a ƙara Naira 130 zuwa 140 ga kowace lita, maimakon 162 zuwa 165 da ake sayarwa a yanzu.

Haka zalika, a watan Mayun 2021, Ƙungiyar Gwamnoni ta Nijeriya ta bada shawarar a mayar da farashin Naira 385, amma gwamnati ba ta karɓi shawarar ba a lokacin.

Irin wannan kwan-gaba-kwan baya da a ke samu na bayanai na matsayar gwamnati kan wannan batu daga dukkan alamu yana kawo ruɗani ga ’yan Nijeriya, inda suke kasa gane inda manufofin tattalin arzikin ƙasar ya sanya gaba. Sai dai kuma wasu na ganin cewa, fadar Shugaba Buhari tana yin taka-tsantsan ne kan batun bisa la’akari da halin ƙuncin da ’yan Nijeriya za su ƙara tsintar kansu, idan aka cire tallafin ba tare yin wani kyakkyawan tanadi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *