Daga UMAR GARBA a Katsina
Kachalla Muhammadu, shugaban dabar ’yan bindiga da ake zargin suna tsare da Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, ya bayyana yadda suka riƙa bibiyar tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya kafin su kama shi.
A cikin wani saƙon murya da majiyar Blueprint Manhaja ta Katsina Times ta samu ya an ji Kachalla Muhammadu na cewa lallai Janar ɗin yana hannunsu tsare a maɓoyarsu.
Majiyar ta ce a cikin saƙon muryar, Kachalla Muhammadu ya tabbatar da cewa Janar Rabe na cikin ƙoshin lafiya a inda suke tsare da shi.
A cewarsa, tun daga birnin Kaduna suke samun bayanai kan motsin Janar Rabe da lokacin da yake fita daga gida.
Kachalla Muhammadu ya bayyana cewa tun farko sun shirya kama Janar ɗin ne a kusa da mararrabar Musawa, inda hanya ke rabuwa zuwa ɓangarori biyu — ɗaya zuwa Musawa, ɗaya kuma zuwa Gidan Mutum Ɗaya. Ya ce sun yi hasashen cewa Janar Rabe zai bi hanyar Gidan Mutum Ɗaya.
Sai dai, a cewarsa, da Janar Rabe ya isa mararrabar, ya zaɓi hanyar Musawa–Matazu. Daga nan ne, Kachalla ya ce, su da wasu abokan aikinsa suka tare shi a hanya, inda suka yi nasarar kama shi.
Wannan sabon bayani da ake dangantawa da Kachalla Muhammadu ya ƙara haifar da zarge zargen cewa akwai wata maƙarƙashiya mai sarƙaƙiya da ta taimaka wajen sace Janar Rabe Abubakar, musamman ganin iƙirarin cewa an daɗe ana bibiyar motsinsa tun daga Kaduna kamar yadda majiyarmu ta bayyana.
