Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas.
Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karɓar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari.
“Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya ɗora daga inda ya tsaya a Legas.”
Sai dai Adebayo ya ce Tinubu ya yi ƙoƙari wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.
“A bayyane yake cewa tattalin arzikin da Shugaba Buhari ya bari ba a tafiyar da shi yadda ya kamata ba, kuma yana cikin mawuyacin yanayi kamar na mara lafiya da aka kai ɗakin jinya. Kamar yadda likita ke buƙatar yin cikakken bincike domin gano matsalar mara lafiyan, haka ma ake bukatar fahimtar matsalar tattalin arziki kafin a fara warkar da ita.
“Abin da Shugaba Tinubu ya yi shi ne ya daidaita marar lafiyan, amma ban tabbatar ko ya kai ga gano matsalar ba. Don haka mara lafiyar ba zai mutu nan da nan ba, amma kuma ba a samo maganin cutar shi ba.
“Ba a gano ciwon da ke damun mara lafiyan ba, amma a matsayinsa na likita, yana ɗaukar wasu matakai. Wasu daga cikin matakan ma sun kara ciwon mara lafiyar, amma sannu a hankali likitan yana samun nasara a wasu ɓangarorin, wanda hakan ke sa wasu su yi tunanin cewa mara lafiyan na kan hanyar warkewa,” inji Adebayo.
