Tushen Zamfara da Zamfarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Blueprint Manhaja ta binciko tare da tattaro bayanai daga wuraren daban-daban dangane da asalin Zamfara da Zamfarawa.

Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata ɗaya daga cikin Banza Bakwai waɗanda ba Hausawan asali ne ba. Dalilin hakan shi ne, ana ganin Bare-bari ne asalin Zamfara. Sarkin musulmi Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira.

To su Zamfarawa sun kafa asalinsu daga Maguzawa maharba waɗanda sun zauna a yankin ƙasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutsen Dala.

A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa Hausawa ne na asali tun can fil azal. Zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa dai asalinsu maharba ne daga Maguzawa. Wataƙila sun samu tasirin Bare-bari a farkon tarihinsu ko kuma a ce Bare-bari na asalin sarautar Zamfara. Tarihin ƙauyen Zamfara ya samo asali ne daga mutum na farko da ya fara zama a garin, daga garin ZAMFARA wanda ake kira da BAWA.

Shi ya sa ake kiran garin da suna Zamfara. Farkon fadar masarautan an rusa ta. Garin ya haɗa iyakoki kamar haka; Rogo sabon gari da Tsohuwar Rogo ta gabas, Bari da Kaduna daga gefen yamma, Kaduna daga Kudu da Gari da Tsohuwar Rogo ta arewa.

Ana ganin Zamfarawan asali wasu irin manya-manyan mutane ne, a takaice dai Samudawa ne. Dakka, sarkin Zamfara na farko kamar dai Barbushe ya ke, mutum  ne mai tsananin girma da ƙarfi da jarumta. Akwai wasu manya-manyan kaburbura guda shida a Dutsi waɗanda aka ce kaburburan sarakunan Zamfara ne na asali. Sabo da girman kaburburansu ana kiransu da kaburburan Samudawa. Ga alamu Zamfarawa asali na da girman jiki sosai.

Birnin Zamfara:
Zamfarawa sun fara kafa garinsu na farko ne mai suna Dutsi a ƙasar Zurmi ta yanzu. Don haka har yau Sarkin Zurmi na amsa sunan Sarkin Zamfara. An ce Zamfarawa sai da suka kwashe shekara bakwai ba su naɗa sarki ba a Dutsi, daga nan sai suka naɗa sarkinsu na farko mai suna Dakka. Don haka Sarkin Zamfara ana masa ta ke da gimshikin gidan Dakka. Sarakuna huɗu ne suka gaji Dakka a Dutsi. Daga nan sai sarauniyar ’Yar Goje.

Daga Dutsi sai Zamfarawa su ka yi tafiyar kamar mil talatin a kan gulbin Gagare kusa da garin Isa na yanzu suka kafa wani sabon gari mai suna Birnin Zamfara. An ce Sarkin Zamfara na bakwai mai suna Bakurukuru ya kafa birnin. Amma wasu masana tarihi sun haƙiƙance cewa sarakuna ashirin da uku 23 ne aka binne a garin Dutsi don haka ba dai sarki na bakwai ba wanda ya kafa Birnin Zamfara. Zamfarawa sun gina garinsu wanda ya haɓaka sosai. Sun katange shi da ganuwa.

Har yanzu akwai kufan tsohon garin akwai rusasshiyar ganuwa mai tsawon miliyan goma-sha-uku da kofofin gari hamsin. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa sun kafa garinsu na biyu wanda ya kasance babbar cibiyar mulkin Zamfara.

Sannan garin ta samu arzikin masarrafofin zamani irin su Makarantun Boko, islamiyya, rijiyoyi da kuma Burtsatse da dai sauransu. Ofishin siyasa ta mata an buɗe ta ne a garin zamfara a shekarar 2007.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *