UNICEF ta yaba wa Gwamna Lawal kan ware biliyan N2.9 don inganta rayuwar al’ummar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya yabawa gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal kan ware zunzurutun kuɗi har naira biliyan 2.9 domin ci gaban shirin kare rayuwar al’umma a jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 30 ga watan Janairu mai ɗauke da sa hannun wakiliyar UNICEF a Najeriya, Cristian Munduate wacce aka miƙa wa ofishin gwamnan kuma aka rabawa manema labarai a yau Asabar.

UNICEF ta bayyana matakin da ɗaukacin ƙananan hukumomi 14 (LGAs) suka yanke na bayar da shawarar ware Naira biliyan 2.9 a cikin kasafin kuɗin su na shekarar 2025 don ayyukan kare rayuwar jama’a a matsayin wani gagarumin ci gaba na ƙarfafa walwalar yara da magance talauci a tsakanin marasa galihu a jihar.

“Wannan nasarar tana nuna himmar gwamnatin Jihar Zamfara don inganta rayuwar masu rauni kuma ta yi daidai da manufofin Kariyar jama’a na jihar”.

“Kamar yadda na tabbatar muku a ziyarar da na yi kwanan nan, UNICEF ta kasance abokiyar haɗin gwiwa wajen tallafawa matakai na gaba, gami da taron ƙarawa juna sani na shugabannin ƙaramar hukumar da masu kula da kare al’umma da aka shirya gudanarwa a ranakun 17 zuwa 20 ga Fabrairu 2025”. Munduate ta Ƙara da cewa.

Hukumar ta UNICEF ta ƙara nuna jin daɗin ta ga salon jagorancin gwamna Dauda Lawal tare da yin kira da a ci gaba da haɗa kai wajen tabbatar da cewa waɗannan alƙawura da aka yi a kasafin kuɗin sunyi tasiri mai ma’ana ga yara da masu ƙaramin karfi a faɗin Jihar Zamfara.

“A madadin UNICEF, ina miƙa saƙon taya murna ga gwamnatin Jihar Zamfara bisa gagarumin ci gaba da aka samu wajen samar da shirin inganta rayuwar yara da marasa galihu a Jihar “. Cristian Munduate ta Ƙara da cewa.