Waƙa: UBANGIJINMU ALLAH (T)

Tare da ABDULHAMID Na MATAZU

  1. Da Sunan Allah na Mai Girma,
    Baitochi ne Zan Tsara ma.
  2. Mabuwayi Kuma Gagara Gasa,
    WANZAJJE tun Kan Kowa Ma.
  3. Bai Haifa Ba Ba a Haifai Ba,
    bai da KINI Allah mai ‘AMA.
  4. Shi ne yake Da Mulkin Sammai,
    har ƙassai Shi sarkin Girma.
  5. Shi ne Muke Nufa Da Buƙata,
    duk kuma Shi ne zai yaye ma.
  6. Allah Shi ke Ba mu ISASSA,
    Shi ke Kawo Har MARDHUN ma.
  7. Sai dai duk CUTAR da Dawa’i,
    in Yaga Dama Yayyaye ma.
  8. Jallah Ya Ba mu Abincin cin mu,
    dats tsuntsaye Dabbobi ma.
  9. Shi yai ZAKI shi yai KURA,
    CINNAKA sauro Da Kunama.
  10. Mai ƊACI bauri Daz ZAQI,
    Har Hamami Tuni na Sallamma.
  11. Shi ya Kamata Ayi wa BAUTA,
    Shi Daya RAK sam Ba a Haɗi ma.
  12. Yi Mai Tarayya ce SHIRKA,
    Bai Karɓa Ranar Ƙiyyama.
  13. In Ka Bi shi Anan Kai Sa’a,
    lahirra can Ba bu Nadama.
  14. Baka Shiga Wuttar Hawiyya,
    a Lahirar Balle su Huɗama.
  15. Abdulhammid Ni NaMATAZU,
    Nayyo Kan Allah Mai Rahma.