Wakilin Ƙasar Sin ya nuna adawa game da tsoma baki cikin harkokin gidan Burundi ta fakewa da kare haƙƙin ɗan Adam

Daga CMG HAUSA

Wakilin ƙasar Sin ya gabatar da jawabi, a gun taron kwamitin kare haƙƙin bil’adama na MƊD karo na 51 a jiya Jumma’a, inda ya yaba da ƙoƙarin ƙasar Burundi, na ingantawa, da kare hakkin bil’adama, ya kuma nuna adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan Burundi, ta hanyar fakewa da kare haƙƙin bil’adama.

Wakilin na ƙasar Sin ya bayyana cewa, a ko da yaushe, ƙasar Sin tana ba da shawarar cewa, ya kamata a kawar da bambance-bambancen da ke tattare da batun kare haƙƙin ɗan Adam, ta hanyar tattaunawa da haɗin gwiwa, tare da adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam.

Ya ce wasu ƙasashe sun yi wa Burundi ƙazafi bisa bayanan ƙarya, sun kuma yi amfani da kwamitin kare haƙƙin bil’adama a matsayin wani makamin siyasa, na tinkarar ƙasashe masu tasowa, da ƙara rura wutar gaba da juna, wanda hakan ba ya taimakawa wajen warware matsalar.

Don haka ya kamata, kwamitin kare haƙƙoƙin ɗan Adam ya kiyaye ƙa’idojin kauce wa wariya da siyasantar da batutuwa, da kuma yin watsi da “ma’auni iri biyu”, kana da mutunta hanyar ci gaban haƙƙin dan Adam da jama’ar Burundi suka zaba da kansu.

Mai fassara: Bilkisu Xin