Mourinho ya buƙaci ’yan wasansa su riƙa faɗuwa da gangan saboda bugun fanareti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin AS Roma, Jose Mourinho, ya shaida wa ’yan wasansa cewar daga yanzu su riƙa yawaita faɗuwa ko da kuwa da gangan ne, don samun qarin damarmakin bugun daga kai sai mai tsaron raga.

A ranar Lahadin da ta gabata, Mourinho ya yi fuskatar da ta kusan kai shi ga rafke alƙalin wasa Daniele Chiffi, saboda hana su damar bugun fanareti, a wasan da Atalanta ta doke su da 1-0.

yayin tankiyar sai dai aka riƙe Mourinho domin hana shi make alƙalin wasan, saboda watsin da ya yi da kiran ya hukunta ɗan wasan Atalanta Caleb Okoli da ya yi wa Nicolo Zaniolo keta, abinda ya sanya jami’in ya kori kocin daga fili bayan daga masa jan kati.

A lokacin da ya ke raddi kan abinda ya faru ne kuma Mourinho ya ce da ɗan wasansa Zanioli bai yi ƙoƙarin miƙewa tsaye ba, a lokacin da aka yi masa ƙeta, to da sun samu damar bugun faneretin da suka cancanci a ba su.

Yanzu haka AS Roma tana matsayi na shida a kan teburin Seria A, da maki 13 bayan buga wasanni bakwai na farko.