FIRS ta ƙaryata batun ta yafe wa wasu kamfanoni haraji

Daga AMINA YUSUF ALI

Mista Muhammad Nami, shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa, (FIRS) ya bayyana cewa, babban aikin hukumar tasu shi ne tattara haraji ba wai su yafe haraji ga wa wani mahaluki mai biyan haraji ba.

Mista Nami ya yi wannan bayani ne ranar Litinin ɗin da ta gabata a yayin da yake mayar da martani ga wani labaran da ya kira da ƙanzon kurege da suke ta yawo a kafafen yaɗa labarai a kan wai hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) ta yafe wa wasu kamfanoni haraji.

Kamfanonin da aka rawaito cewa wai hukumar ta yafe wa harajin sun haɗa da: Kamfanin Ɗangote Sinotruck Limited, kamfanin Lafarge, kamfanin Honeywell, da ma sauransu. Inda rahotannin suke ikirarin wai hukumar FIRS da sauran hukumomin gwamnatin sun yafe wa kamfanonin haraji na tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021. Abinda ya kama zunzurutun kuɗi har Naira tiriliyan N16.

A cikin jawabin wanda yake dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman a vangaren yaɗa labarai, Johannes Oluwatobi Wojuola, Mista Nami ya ƙara da cewa, sam hukumar FIRS ma ba su da iko ko hurumin yafe wa wasu ‘yan kasuwa ko kamfanoni haraji a Nijeriya.

A cewar sa, akwai hukumomin da suke da alhakin yin wannan. Sai dai kuma a cewar sa, akwai wasu dalilai da za su iya sa gwamnati ta iya waccan yafiya ta haraji da suka haɗa da, don bunƙasa ƙananan kamfanoni na ƙasa, bunƙasar tattalin arziki, samun yardar ‘yan kasuwa.

Sannan ya ƙara da cewa, a halin yanzu ma kamfanonin da suke morar hutun harajin da aka ba su su ma sun kusa dawowa su cigaba da biyan harajin daruruwan biliyoyin Naira.