Buƙatar kafa rundunar ’yan sandan jihohi

Bayan kwashe shekaru masu yawa, majalisar wakilan Nijeriya ta yi nisa wajen aiki a kan ƙudurin dokar da za ta halatta kafa ‘yan sandan jihohi domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka adabi ƙasar.

Da alamu dai an kama hanyar kawo ƙarshen tirje-tirje da ma tayar da jijiyar wuya, a kan wannan batu da aka kwashe lokaci mai tsawo ana ja-in-ja a kan halaccinsa ko akasin haka.

Sakamakon Matsalar tsaro da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan, gwamnonin jihohin Arewa 19 ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da kuma Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC) sun yi kira da a kafa ’yan sandan jihohi.

Gwamnonin da sarakunan, waɗanda suka yi wannan kiran a ƙarshen taron da suka yi a Abuja, sun bayyana cewa, ’yan sandan jihohi za su taka rawar gani wajen magance matsalolin tsaro a yankin Arewa da sauran sassan ƙasar nan. Baya ga haka, babu shakka a halin yanzu ƙasar na fama da matsalar ’yan bindiga, tada ƙayar baya, garkuwa da mutane da sauran nau’o’in laifuka.

A cewar shugaban ƙungiyar NGF kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, taron ya yi nazari kan matsalar tsaro a yankin Arewa da sauran al’amuran da suka shafi cigabanta, inda aka yanke shawarar goyan bayan gyaran kundin tsarin mulki na 1999 domin ɗaukar nauyin kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, Abubakar Sani Bello na Jihar Neja, da Darius Dickson Ishaku na Jihar Taraba duk sun halarci taron. Sauran sun haɗa da mataimakan gwamnonin jihohin Adamawa, Benuwai, Nasarawa da Jigawa.

Sarakunan gargajiya da suka halarci taron sun haɗa da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi; Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, da sauransu.

Muna yaba wa gwamnoni da sarakunan Arewa bisa yadda suka bi sahun sauran ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa wajen ƙoƙarin ganin an magance matsalar rashin tsaro. Kiran da suka yi na kafa rundunar ’yan sandan Jihohi, a matsayin hanyar magance matsalar rashin tsaro, ya biyo bayan waɗanda wasu fitattun ’yan Najeriya da qungiyoyin al’adu da suka haɗa da Afenifere, Ohanaeze Ndigbo, Pan Niger Delta Forum (PANDEF), da Middle Belt Forum (MBF), suka yi a baya.

Dangane da ƙaruwar rashin tsaro da aikata laifuka a dukkan sassan ƙasar nan, an ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman kafa sabuwar hanya kan ‘yan sandan Nijeriya. Magoya bayan kafa ’yan sandan jihohi na ganin hakan zai rage yawaitar rashin tsaro a ƙasar.

Sun kuma yi nuni da cewa tsarin ’yan sanda na tsakiya na yanzu ba zai iya ba kuma ba zai magance matsalar rashin tsaro a tarayyar Nijeriya ba. Sun yi ta rarrashin cewa abu ne mai wuya tsarin ’yan sandan da ake da shi a halin yanzu ya yi aiki yadda ya kamata a ce ƙasa mai girman Nijeriya daga Abuja.

Ga alama gazawar tsarin ‘yan sandan ƙasa abu ne wanda ba za a iya voyewa ba. Wataƙila wannan shine dalilin da ya sa kira ga ‘yan sandan jihohi ke ƙaruwa tare da samun sabbin kiraye-kiraye a faɗin ƙasar. Wani ɓangare na shawarwarin taron ƙasa na 2014 shi ne samar da ’yan sandan jihohi. An dai yi ittifaƙin cewa aikin ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen rage yawan aikata laifuka a ƙasar.

Tunda kowane laifi na gida ne, samar da tsarin ’yan sanda na jiha, zai daƙile rashin tsaro, idan an sarrafa shi da isassun kayan aiki. Kasancewa kusa da jama’a, jami’an ‘yan sandan jihohi suna da damar sanin kowa da kowa. A lokaci guda, hakan zai amsa ga kiran gaggawa ga al’amuran tsaro.

Tare da isassun matakan bincike na hukumomi, za a kafa ’yan sandan jihohi yadda ya kamata. Hatta tsarin ’yan sanda na yanzu ba za a iya cewa ba lalle ya haɗa kafaɗa da wannan sabon tsarin ba. Idan aka yi la’akari da gazawar da ke tattare da tsarin ‘yan sanda na zamani, lokaci ya yi da za a ba ‘yan sandan jihohi dama.

Ma’ana, Nijeriya za a iya cewa ta isa ga jahohi da sauran sassan ’an sanda. Muna goyon bayan aikin ’yan sanda na jiha da sauran matakan ’yan sanda a ƙananan hukumomi da ma matakan al’umma. Wataƙila wannan ita ce hanya mafi dacewa don tunkarar dodo na rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.

A shekarar 2012, a matsayin hanyar tinkarar ƙalubalen tsaron ƙasar, gwamnonin jihohi 36 sun yi kira da a kafa ’yan sandan jihohi. Mun yi imanin cewa gwamnoni za su iya yin aiki tare don tabbatar da cewa an kafa ‘yan sandan jihohi. Kafa ƙungiyoyin tsaro a yankin, irin su Amotekun a Kudu maso Yamma da Ebube-Agu a Kudu maso Gabas yana ƙara jaddada muhimmancin aikin ’yan sandan jihohi.

Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba buƙatar kafa ’yan sandan Jihohi ta kuma ba ta kulawa cikin gaggawa. Gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na iya fara ɗaukar matakin kafin ya bar mulki.

Inda ya tsaya, ya kamata ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun siyasa a zaɓen 2023 su ɗauki buƙatar a matsayin babban fifiko. Taɓarɓarewar ƙalubalen tsaro ya sa buƙatar kafa ’yan sandan jihohi ba za ta kau ba. Kira ne da kada gwamnati ta yi watsi da ita.

Muna kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Majalisar Dokoki ta Jiha da su gabatar da muhimman dokokin da za su kai ga kafa rundunar ’an sandan jihohi. Ajanda ce da ba za a iya ɗage ta ba.