Ziyarar musamman: Yadda masha’a ta ragu a garin Tafa

*Yanzu gidan karuwai kashi 30 ne a garin
*Mu biyar muka fara kafa garin, inji Goran Tafa
*Ashe ’yan asalin Kano suka kafa garin
*Gwamna El-Rufai ya yi watsi da mu, cewar mazaunan Tafa

Daga MOHAMMED ALI a Tafa

Garin Tafa yana cikin Ƙaramar Hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna ne, inda ya ke da nisan kilomita 161 daga Garin Kaduna akan hanyar zuwa Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, wanda kuma kilomita 41 ne tsakaninsa da Abuja ɗin. Tafa ya yi shuhura da fice, musamman saboda kasancewarsa wani wajen yada zango ga direbobi masu lodin manyan motoci ƙurar Tirela.

Sai dai kuma a shekarun baya garin ya yi ƙaurin suna wajen aikata masha’a sakamakon karuwai da ake zargin cewa, sun mamaye shi, waɗanda yawancinsu ake ganin mu’amularsu da direbobin motocin ce ta sanya su share wuri su zauna a garin., inda har akan ce, yawan gidajen karuwai a garin ya kai na gidajen matan aure yawa. Har ta kai ta kawo har wasu na yi wa garin take da ‘garin shege da shegeya, idan ka ɗan halak, baƙo ne’.

To, amma a ziyarar da Wakilin Blueprint Manhaja, MOHAMMED ALI, ya kai garin Tafa a kwanan nan, ya gano cewa, al’amura sun fara sauyawa, kuma har ya yi gamo da kar na sanin asalin garin da yadda ya kafu a lokacin su Sardauna.

Yadda aka kafa Garin Tafa:

“Ainihin sunan Tafa ya samo asali ne daga wani kogi mai suna Kogin Tafa, wanda yake kusa da garin, inda a lokacin da iyayenmu da mu muka zo wurin, wato inda Tafa take yanzu. A lokacin babu komai sai ƙungurumin daji, ba gida ko ɗaya, balle bil adama. Mu masunta ne da muka taso daga can garin Bunkure na Jihar Kano a 1965 da nufin yin su, wato kamun kifi a wannan rafi mai suna Tafa. Ba gida ko ɗaya, sai daji kawai, wanda duk cikin dajin babu komai sai namun daji iri-iri.”

Yadda wasu ke ciki a garin Tafa

Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin Mai Girma Malam Shehu Sulaiman, Goran Tafa, wato kamar Dagaci kenan, a lokacin da yake zantawa da Wakilan Blueprint Manhaja a fadarsa da ke Tafa a cikin yankin Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, inda ƙara da cace, su biyar suka taso daga Kano, don yin sana’ar su ta kamun kifi a 1965, yana mai cewa, “shekara ɗaya kafin a kashe su Sardauna muka zo, don yin su.”

Ya ce, da farko, sun ya da zango ne a wani gari mai suna Panda na cikin Keffi, inda suka yi shekara huɗu a garin. Daga nan suka zarto zuwa Kubaca ta Kagarko, daga nan kuma a 1979 suka iso wani babban daji kusa da Kogin Tafa a matsayin masunta. “A lokacin mulkin Shagari,” inji shi. To, idan sun yi kamun kifi, sai su je wata kasuwa mai suna Kasuwar Isa a can gaba da rafin Tafa su kwana.

A cewar Goran Tafa, da tafiya ta yi tafiya sai suka ga ya kamata su samu wurin rayuwa na din-din-din, inda suka yanke shawara su tuntuɓi Sarkin Kagarko na wancan lokacin.

To, sai shi Sarkin ya aika da su zuwa wajen Sarkin Minna, wanda ya ba su izinin su zaɓi wurin da zai yi musu daɗin zama. Sai suka dawo dajin kusa da Rafin Tafa, suka yada zango a wurin, suka fara gina mazauni.

A kwana a tashi, suka share fili sosai bayan sun yi aiki tuƙuru, suna sassare bishiyoyi da itatuwa. Bayan kwana da kwanaki, suka yi nasarar share katafaren wurare a dajin, suka mayar da su filaye, suka gig-gina muhallinsu. Haka aka kafa Garin Tafa.

Ya tuna da cewa, cikin ikon Allah da kuma roƙon shi, sai suka soma samun baƙi masu buƙatar wurin yin gini, don zama.

” Ai mu tunda muna neman wuri ya zama gari, sai muka yay-yanki filaye, mutane na ta gine-gine, suna zama. Kafin wani ɗan lokaci, dajin ya kau, alƙarya ta ginu. Wannan dajin, shine garin Tafa a yau, wanda mu ne muka kafa shi, mu biyar kacal, yau kusan shekaru 50 kenan,” inji shi kan yadda garin Tafa ta kafu.

Da aka tambaye shi ko me ya sa garin Tafa ya yi ƙaurin suna, musamman game da mata masu zaman kansu, sai Malam Shehu ya yi bayanin cewa, lamarin ya samo asali ne daga garin Gauraka da ke Jihar Neja akan iyakarta da Jihar Kaduna, inda a wancan lokacin ya yi mummunan qaurin suna a kan alfasha iri-iri, kamar sata, karuwanci, shaye-shaye da sauransu.

To, da abin ya kai intaha, ya ƙazanta ainun, sai Gwamnan Jam’iyyar NPN na Jihar Neja a wancan lokacin (1979-1983), wanda kuma shine Sarkin Suleja na yanzu, wato Alhaji Muhammad Auwal Ibrahim, ya bayar da umarni a yi rusau, a kuma kori karuwai da ‘yan daudu da ire-irensu gabaɗaya, su fice daga garin, su san inda dare ya yi musu.

“To, ina suka dosa mafi kusa da su, kawai sai suka gangaro wannan garin namu, Tafa. Duk da shike muna begen baƙi, gari ya cika, amma gaskiya ba ta irin wannan yanayi da tsari ba,” inji shi, amma to yaya suka iya?

Dole suka rungumi baƙin, suka kuma rungumi ƙaddara, yana mai cewa, “babu abin yi, sai muka duƙufa roƙon Allah, ba dare ba rana, da muka farga lamarin na son ya rikiɗe zuwa kamar yanayi irin na Gauraka, garin da aka tarwatsa, saboda aikin assha,” inji shi.

“Alhamdulillahi,” inji shi, al’amarin ya sauya, tunda an samu sauƙi yanzu. Babu tashin hankali a Tafa, matasa ba sa fitina, haka ma karuwai kowacce ta kama sana’a, don neman na kanta, musamman sayar da abinci da wanki da guga, kuma da yawa sun bar garin, ba kamar da ba. Babu ‘yan daudu, haka shaye-shaye tsakanin matasa sun ragu ainun. Babu faɗace- faɗace tsakanin matasa ko mazauna gari kamar a wasu wurare.

Ko da shike bincike ya nuna, yanzu akwai gadajen mata nan da can a garin Tafa, amma ba su kai kashi 30 bisa 100 ba, ba kamar a baya can, inda kusan kashi 60 bisa 100 gidaje da wuraren assha sun mamaye ko‘ina. Yau, akwai manyan ma’aikatan gwamnati a Tafa. Akwai manyan ’yan kasuwa, ga kuma manya-manyan malaman addinin Musulunci da manyan fasto na addinin Kiristanci.

“Saboda haka, mun gode Allah da ya karɓi addu’armu. Yau a Tafa, babu yaren da babu, akwai Hausawa da Yarabawa da Fulani da Ibo da Kanuri da Gwarawa da Katafawa da al’umma daban-daban da suka fito daga sassan Nijeriya da dama, kuma ana zaman lafiya, babu tsangwama, ana zaune lafiya Musulmi da Kirista, idan banda ɗan abin da ba za a rasa ba, wannan kuma yau da gobe ce sai Allah, kamar yadda za a samu a wasu wurare,” inji shi dagacin na Tafa.

Yadda gwamnati ta yi watsi da su:

Ko shakka babu, ana kyakkyawar zamantakewa a Tafa. Sai dai Malam Shehu ya yi kukan cewa, ba su da hanyoyi da magudanan ruwa da ruwan sha a garin, kuma gwamnati ba ta sa su cikin tallafin da ta kan yi wa al’umma a jihar ba.

“Don haka, Ina kira ga gwamnatin mai Girma Gwamna, Alhaji Nasiru El-Rufa’i, da ya tuna da mu wajen tallafin da gwamnatinsa ke yi duk lokacin da tsarin ya taso.

Mu mutanen Tafa, masu bin doka da oda ne, muna da masu sana’oi iri-iri, kuma masu shi suna biyan haraji tun daga karamar hukuma har zuwa jiha. A kuma bai wa matasanmu aiki.

Akwai masu ilimin difloma da NCE har masu digiri muna da su,” inji shi.
Malam Shehu ya ce, ita wannan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna an fara gina ta ne a 1981, inda aka fara zuba kwalta a 1982, yana mai cewa, yau babban titin duk da yana neman gyaran Gwamnatin Tarayya, yana da tasiri musamman ga direbobin tireloli da tanka-tanka, waɗanda suke ya yin zango a koyaushe a Tafa, kuma kullum abun ƙaruwa yake yi tunda ya zame musu al’ada, yana mai cewa, “amma kuma zuwa suna yada zango da jerin motocin nasu, alheri ne a nan Tafa, saboda a nan za su ci abinci, su kwana a loja-loja, kuma duk biya suke yi.

*To, ka ga wannan riba ce gare mu. Kuma ka ga akwai babban defo, inda wasu da yawa ke faka manyan motocin nasu, kuma duk rana suna biyan kuɗin shiga, wanda ake amfani da shi.”

Malam Shehu ya ƙara da cewa, saboda ƙaurace wa barazanar ‘yan ta’adda ne da suka addabi wurare, kamar Birnin Gwari na Jihar Kaduna da Jihar Nasarawa da kuma Jihar Neja, ya sa direbobin suka fi amincewa da Tafa, yana mai ƙarawa da cewa, “idan da duk waɗannan jihohi da wasu wurare cikin Jihar Kaduna za su samu kyakkyawan tsaro daga hare-haren ‘yan bindiga da zaman lafiya kamar Tafa, da Gwamna El-Rufa’i da duk sauran al’umma sun riƙa tafiyar da harkokinsu na yau da kullum a tsanake, kuma su yi barcinsu idanuwansu a rufe.”

Ya tuna tun kafa garin Tafa, ba su fuskantar fitina ko tashe-tashen hankali ba, idan banda wata gobarar tanka da ta jefa mutane cikin ruɗani da tashin hankali, “amma a ce fitina ko faɗace- faɗace a tsakanin al’umma, babu a na,” inji shi.

Sai dai ya gode wa Gwamnatin Jihar Kaduna da ta gina musu asibiti da makarantun firamare da na sakandare a garin, kuma suna cigaba har yanzu. Amma Goran ya yi takaici yadda wasu jami’ai za su zo wurinsu, su ce wai su daga Abuja ko daga Gwamnatin Kaduna ko Ƙaramar Hukuma suke, su ba su fom su ciccika da nufin za a kawo musu tallafi, amma da zarar sun tafi, ba su ƙara ganin su. Haka zalika ya ce, “ko ɗaukar matasa aikin soja, ‘yan sanda ko sojan ruwa, sibil difens, babu wani matashin Tafa da ya taba samu.

Halin da wasu hanyoyin Tafa ke ciki

“Don Allah wannan abu da dadi? Ai kamata ya yi a tafi tare da mu a cikin ko wani tsari na gwamnati, tunda mu ma ‘yan Najeriya ne.”

Ya danganta zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa a Tafa ga addu’ar kawar da masifa, wanda Musulmi da Kiristoci suke ta yi a kullum, yana mai cewa, “ba inda ake addinin Musulunci a duk ƙananan hukumomin Jihar Kaduna kamar yadda ake gudanarwa a Tafa. Haka ma addinin Kirista, kuma an zame ɗaya, ana ta ibada duk mutane ba su san da wannan ba, amma sai su yi ta aibata Tafa. Su shigo mana su gani “.

Ya ce, yau a Tafa akwai manyan masallatan Juma’a guda biyar da masallatan khamsussalawat sama da 75. Akwai kuma makarantun tsangaya 80, ga kuma makarantun islamiyya ta ko’ina ciki da kewayen garin. Sai kuma coci-coci sama da 20, inda Kiristoci yawancinsu ‘yan Kudu, suke gudanar da addininsu.

Ya ƙara da cewa, “kuma duk daren Juma’a, ana sauke Alƙur’ani mai girma, don zaman lafiya ya ɗore, kuma alhamduLillahi.”

Sai ya gode wa shugabannin addinan biyu, Musulunci da Kirista, saboda abin da ya kira “jihadin da suka yi, don tabbatar da zaman lafiya a Tafa da cigabanta.” Ya yi kuma kira ga jama’ar garin da su ci gaba da irin wannann kyakkyawan zamantakewa a tsakaninsu.

Idan ka zagaya cikin garin Tafa yana da wuyar tafiya, amma yana da muhimmanci, saboda mutum zai gane yadda yanayin garin yake da yadda mutane suke rayuwarsu da irin tunaninsu.

A gaskiya ne, al’ummar garin masu son tsafta ne da neman na kansu, amma sai dai sam ba su mori ababen more rayuwa ba, musamman hanyoyi, ko’ina ka zaga caɓi ne kawai da laka idan an yi ruwan sama.

“Mu dai a nan, mun dogara ga Allah ne kawai, babu komai na jin daɗin ɗan adam. Ba mu da hanyoyi, ba mu da magudanar ruwa. Kai ga su nan ba iyaka.” Wannan kalami ne daga bakin ɗaya daga cikin dattawan Tafa, Malam Garba Wanzam, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Acaɓa, wato Zaman Lafiya Okada Association, Tafa, a lokacin da yake tofa albarkacin bakin shi a kan Tafa.

Mallam Garba ya tuna cewa, “a lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya zo kamfen ɗinshi a Tafa, mutanen da suka tarbe shi, ba iyaka, mata da maza, manya da yara, har matasa suka nuna ma sa da tawagar shi bajinta iri-iri a kan babura da tireloli da Keke Napep.

Wasu matasan ma, suka kwan-kwanta a kan kwalta, suna kusumbolo, ana musu kida suna ta nuna bajintarsu, duka saboda murnar zuwan El-Rufa’i.

“A lokacin gwamnan yayi matuƙar farin ciki, kuma ya yi mana alƙawuran abubuwan jin daɗi iri-iri, kafin su koma. Ya kuma ci zaɓe, amma tun hawarsa kujerar gwamna, mu ba mu taɓa cin moriyar wani abin a-zo-a-gani daga gwamnatinshi ba. Makaranta da asibiti, tun kafin hawansa ne aka yi mana.

“To, duk da haka muna ƙaunar shi ɗari bisa ɗari. Amma gaskiya ya zo ya yi mana wani abu kafin ya sauka ko don irin zaman lafiyar da ya ɗore a Tafa da bin doka da oda, ba kamar a wasu wurare ba.”

Garba Wanzam, wanda ya ce, shekararsa 20 a Tafa. Ya cigaba da cewa, duk yadda mutane suke yi wa Tafa mummunan fahimta, to idan sun shiga cikin garin za su yi mamakin yadda yanayin garin da rayuwar al’umma suke. “Tsarkakakkiyar rayuwa ce, ba kamar yadda wasu suke da jahilcin fahimta ba,” inji shi.

Haka shi ma Mallam Lawan Mai Wanki da Guga, ya nuna baƙin ciki yadda gwamnati ta manta da Tafa, duk da halin dattakun mutanen garin masu bin doka da odar gwamnati, masu kuma zaman lafiya.

Ya ce, Gwamna El-Rufa’i ya zo ya yi musu kamfen, suka yi mishi alƙawarin ƙuri’u, yayi musu alkawarai iri-iri, ya je ya ci zaɓe, amma a cewarsa, tunda ya tafi, bai tava waiwayo su ba, sai dai idan hanya ta biyo da shi wucewa zuwa Abuja, yana mai ƙarawa da cewa, “duk cikin ƙananan hukumomin Jihar Kaduna, babu inda Gwamna El-Rufa’i ya samu goyon baya kamar irin yadda ya samu a tamu Ƙaramar Hukumar ta Kagarko, amma sam, bai damu da mu ba, ko don mu talakawa ne?”

wWata hanya a garin Tafa

Haka za a yi ta ji idan mutum ya zagaya cikin garin Tafa, wato koke-koke akan buƙatun ɗan adam na yau da kullum, kamar yadda Malam Ɗan Bayero da Malam Saminu Tafa da Malama Mairo Iliya da Mr.

Nicholas Ndubisi da Mr. Ola John da sauran wasu mazauna garin Tafa suke ta kokawa. Duk da gudun kar su ɗauki “babban shugaba a matsayin wanda ba ya cika alƙawari, ko ɗan siyasa wanda ya yi musu ƙarya.”