Matsayin kunya a rayuwar Bahaushe

Manhaja logo

Idan mai karatu na biye da mu a wasiƙunmu na baya mun yi magana ne akan matsayin kunya a al’adar Bahaushe sannan daga bisani kuma muka gangaro muka duba asalin waɗanda shi wanna al’adar tafi shafa a cikin al’umma.

Yadda kunya ta kasance a rayuwar Bahaushe jiya, ba haka ta ci gaba da kasancewa a yau ba, domin kuwa ta samu ’yan sauye-sauye, sakamakon mu’amalar wasu da wasu baƙin ƙabilu da suka shigo ƙasar Hausa, suka mamaye. Manyan al’umma da suka fi tasiri a kan rayuwar Bahaushe su ne Larabawa da Turawa.

Larabawa:

Larabawa da suka shigo ƙasar Hausa, sun kawo Addinin Musulunci, wanda ya fidda rayuwar Bahaushe daga duhun kai na Addinin Maguzanci zuwa haske na Addinin Musulunci. Don haka aƙidun Balarabiyar al’ada wacce ta dogara kacokan kan koyar alƙur’ani da sunnah ta yi tasiri a rayuwar Bahaushe.

Akwai al’adun Bahaushe da aka watsar saboda sun sava wa ƙa’ida, akwai kuma waɗanda aka cigaba da runguma sabo da sun dace da ƙa’ida. Cikin waɗanda aka cigaba da rungumar ‘kunya’ na ciki. Dalili kuwa yana cikin koyarwar Alƙur’ani da Hadisi kamar yadda ayoyi suka tabbatar da hakan a baya. Don haka mu’amalar Bahaushe da Balarabe kyawawan sauyi aka samu cikin rayuwar Hausa.

Kunya a Addinin Musulunci:

Addinin Musulunci shi ne addinin Bahaushe ya karɓa bayan fita daga duhun kai (Maguzanci) Musulunci ya yi tasiri sosai kan rayuwar Bahaushe wajen jaddada nasa bin umurni da hani na Allah (SWT) da kuma bin tafarki Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, (SAW). Kunya abu ne mai Muhimmanci da matsayi a Musulunci. Wannan ya tabbata ne cikin wasu ayoyin Ƙur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) kamar haka:

Allah maɗaukakin sarki ya ce, “Lalle wannan yana cutar da Annabi, to yana jin kunyarku alhali kuwa Allah ba ya jin kunya da gaskiya…” (Ƙur’ani 33:53).

Haka kuma cikin alƙur’ani mai girma, an kawo ƙissar Annabi Musa, wajen da taimaka wa ’ya’yan Annabi Shu’aibu shayar da dabbobinsu. Saboda wannan taimakawar ne mahaifinsu ya umurce su, da su kirawo ya zo, zuwa gare shi. Allah (SWT) ya ce, “Daga Abu Sa’idul Khudri, Allah ya ƙara masa yarda ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya fi kowa jin kunya, mukan gane abin da ba ya so ne ta fuskarsa”.

Turawa:

Kamar yadda zuwan Balarabe ƙasar Hausa ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe, haka zuwan Turawa. Duk da cewa zuwan Bature ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe ta samar da wasu kayayyakin more rayuwa da, da can baya bai san su ba, amma kuma sun kawo tarnaki ga wasu al’adun Hausawa, waɗanda daga cikin su akwai “Kunya”.

Zuwan Turawa ƙasar Hausa, ya sa Bahaushe na ɗaukar wasu al’adunsa, a matsayin rashin wayewar kai musamman masu ilimin boko. Don haka za a taras daidaiku ne daga cikin mata a yau ke iya kinayar sunayen mazajensu. Hakazalika voye sunan ɗan farko ma ana ɗaukarsa rashin wayewa don haka yawancin mata na kiran ’ya’yan fari da sunayensu.

Haka kuma ’yan matan zamani kan furta wasu kalamai da be kamata ba musamman a cikin fina-finai amma kunya ba ta kama su. Raye-raye tsakanin maza da mata duk abubuwa ne na kunya amma a yau ya zama ruwan dare a al’umma. Don haka al’ada da addini ba su amince da rashin kunya, kuma duk mara kunya ana ɗaukarsa ne a matsayin mutumin banza.

Kuma duk abin da ya yi ba zai zamo abin mamaki ba. A faɗin wani hadisi Manzon Allah Tsira da amince Allah su tabbata a gare shi na cewa

“Yana daga cikin abin da mutane suka riska daga kalaman Annabawan farko, idan ba ka da kunya, ka yi abin da ka ga dama.”

Wassalm. Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.