Ƙaruwar bashin da ake bin Nijeriya abin damuwa ne

Manhaja logo

Ga duk mai bibiyar kafafen yaɗa labarai zai ji cewa, Nijeriya ta ƙara shiga tsaka mai wuya kan yawan bashin da ƙasar ke ƙara ciwo wa kanta.

Yawan bashin da gwamnatin Nijeriya ta ciyo ya qaru zuwa Naira tiriliyan 42, a cewar Ofishin Kula Basuka na Ƙasa (DMO).

Ofishin ya cewa a cikin wata uku, daga Maris zuwa Yuni na 2022, Nijeriya ta ciyo ƙarin bashin Dala biliyan uku, wanda ya sa abin da ake bin ta ƙaruwa zuwa Dala biliyan 103.31 daga Dala biliyan 100.

Hakan na nufin idan aka raba wa ’yan Nijeriya mutum miliyan 200 bashin, kowannensu zai biya Naira 210,000.

Idan aka kwatanta da kasafin Naira tiriliyan 19.97 na shekarar 2023 da Shugaba Buhari zai gabatar a watan Oktoba, bashin ya ninka kasafin sau biyu da ɗoriya.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce, “basukan da ake bin mu sun ƙaru me saboda rancen da Gwamnatin Tarayya ta karɓa domin cike giɓin da aka samu a kasafin 2022 da kuma basukan da gwamnatocin jihohi da Birnin Tarayya suka ciyo,” a cikin wata ukun.

DMO ya bayyana cewa, a tsawon watan ukun basukan cikin sun ƙaru zuwa Naira tiriliyan N26.23 (Dala biliyan 63.24); amma ba a samu ƙari na ƙasashen waje ba daga Naira tiriliyan 16.61 (Dala biliyan 39.96).

A ƙarshen watan Maris na 2022, Naira tiriliyan 24.98 (Dala biliyan 60.1 ne bashin da ake bin gwamnatocin a cikin gida.

DMO ta bayyana cewa fiye da rabin basukan da gwamnatocin suka ciyo an karɓe su ne ta hanyar jingina ko ayyukan haɗin gwiwa.

“Sama da kashi 58 na basukan ƙasashen wajen kan karɓo su ne ta hanyar jingina, Lamuni ko domin aiwatar da ayyukan haɗin gwiwa.

“An karɓo su ne daga masu ba da rance na ƙasa da ƙasa irin su Bankin Duniya, Asusun Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, Bankin Afrexim, Bankin Raya Ƙasashen Afrika, da ƙasashen Jamus, China, Japan, India da Faransa.

Ta ci gaba da cewa, har yanzu yawan basukan na kashi 23.06 cikin 100 bai wuce misali ba idan aka kwatanta da yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin ƙasar.

Ta bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta duƙufa wajen ɓullo da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma rage basukan da ake binta.

A ainihin gaskiya, ya kamata gwamnatin Nijeriya ta san halin da ta ke ciki a game da laruwar bashin da ake bin ƙasar, domin hakan ya iya jawo wata matsalar, bayan matsalolin da daman ƙasar ke fuskanta.

Daga Ɗan Ƙasa Mai Kishin Ƙasa, 08141306201.