Wakilin Sin ya zargi kan yadda Amurka ke tsare mutane ba bisa doka ba

Daga CMG HAUSA

Wakilin ƙasar Sin ya zargi kan yadda ake tsare mutane ba bisa doka ba a Amurka a yayin taron yin musayar ra’ayoyi da kwamitin kare hakkin ɗan Adam na MƊD karo na 51 da hukumar kula da batun tsare mutane ba bisa doka ba suka shirya tare a ranar 19 ga wata.

Wakilin Sin ya bayyana cewa, a shekarar 2021, Amurka ta tsare baƙin haure sama da miliyan 1.7, kuma a ciki akwai 80%, ciki har da yara dubu 45 da aka tsare su a gidajen yari masu zaman kansu.

Bugu da kari, yanayin irin waɗannan gidajen yari masu zaman kansu, ba su da kyau.

Sakamakon haka, an lalata lafiyar mutanen da aka tsare, har ma a kan samu matsalolin take haƙƙin bil-adam a kullum a waɗannan gidajen yari masu zaman kansu.

Haka kuma, a mafakar Brisburgh kaɗai, an tsare yara kusan 5000.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, har yanzu Amurka tana tsare da mutanen da ba a hukunta su bisa doka ba a kurkukun Guantanamo.

Saboda haka, a watan Janairun bana, ƙungiyar kwararru ta musamman ta fitar da wata sanarwa inda ta nuna cewa, kurkukun Guantanamo ya kasance kamar wani “Tabo dake kan alƙawarin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na tafiyar da mulki bisa doka”.

Ƙungiyar ta kuma nemi gwamnatin Amurka da ta kawo ƙarshen “mummunan babi na cin zarafin haƙƙin ɗan Adam kamar yadda take so”.

Ɓangaren Sin ya buƙaci Amurka da ta sanya idonta kamar yadda ya kamata kan matsalolin take haƙƙin bil Adama da suke faruwa a ƙasar Amurka, ta dakatar da tsare ’yan gudun hijira ba bisa doka ba da sauran al’amuran cin zarafin haƙƙin dan Adam.

Haka kuma ya kamata ta biya kuɗin tallafi da ma diyya ga waɗanda aka take haƙƙinsu.

Mai fassara: Safiyah Ma