Wane dalili ke hana matasa rungumar noma?

Assalam alaikum. Wani binciken masana da Ƙungiyar Heifer International ta gudanar ya bayyana cewar, manoma a nahiyar Afirka basa samun damar da ta dace na amfani da sabbin na’urorin zamani wajen bunƙasa aikin noman da suke yi, abinda ke hana su samun ci gaban da ake buƙata.

Rahotan ƙungiyar Heifer International da aka yi nazari a ƙasashe 11 da ke nahiyar Afirka ya gano cewar rashin samun na’urorin zamani wajen tafiyar da harkar noman da kuɗaɗe da kuma horarwar da ta dace na matuƙar illa ga ɓangaren noman da samar da abinci.

Rahotan da aka yiwa laƙabi da ‘makomar aikin noma da kuma rawar da matasa ke takawa wajen amfani da na’urorin zamani‘ ya biyo bayan tambayoyin da aka yiwa matasa kusan 30,000 tare da ɗaruruwan manoma da ƙungiyoyin su a ƙasashen da suka haɗa da Habasha da Kenya da Nijeriya da Ghana da Senegal da kuma Tanzania.

Binciken ya gano muhimmancin tallafawa matasa da kuɗaɗe domin rungumar aikin noman domin samar da ayyukan yi da farfaɗo da hanyoyin samar da abinci wanda annobar Korona ta yiwa matuƙar illa.

Adesuwa Ifedi, mataimakiyar shugabar Heifer International tace nahiyar Afirka da ke ɗauke da tarin matasa na buƙatar inganta vangaren noma wajen zuba jarin da zai janyo hankalin matasa sun rungumi aikin domin wadata jama’a da abinci.

Ifedi ta bayyana takaici da yadda ake samun koma baya wajen samar da kuɗaɗe da kuma zuba jari da horarwar da ta dace wajen samar da manoman da ke amfani da sabbin dabarun zamani domin bunƙasa noman da ake buƙata.

Rahotan binciken ya ji ta bakin matasa 29,9000 da ƙananan manoma 299 da kuma waɗanda suka ci gajiyar fara noman 110 domin gano matsalolin da ake fuskanta.

Ifedi tace sanya matasa da dama cikin aikin noma da samar da abinci na da matuqar muhimmanci wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasashen Afirka da kuma inganta rayuwar manoman.

A ƙarshe rahotan ya bada shawarar yadda za a shawo kan matsalolin da aka fuskanta da suka haɗa da samun jari da horo da fili domin gudanar da aikin noman da kuma rungumar amfani da na’urorin zamani ga ƙananan manoma a farashi mai rahusa.

Daga Ahmad Musa, 09070905293.