Gwamnan Kano ya rushe shugabancin Hukumar Alhazai tare da naɗa sabo

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rushe shugabancin Hukumar Alhazai ta jihar, inda nan take ya maye gurbin waɗanda aka sauke da wasu don tabbatar da an yi Hajji mai inganci a bana.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babban sakataren yaɗa labarai na Gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, da ya fitar a daren ranar Litinin bayan shan rantsuwar kama aiki.

Sanarwa ta ce, waɗanda sabon Gwamnan ya naɗa matsayin waɗanda za su shugabanci hukumar sun haɗa da Alhaji Yusuf Lawan matsayin ciyaman, sai Babban sakataren hukumar watau Alhaji Laminu Rabi’u.

Sauran mambobin hukumar su ne Shiek Shehi Shehi Maihula a matsayin Mamba, Ambasada Munir Lawan, Shiek Isma’il Mangu, Hajiya Aishatu Munir Matawalle, sai Dr. Sani Ashir.

A ƙarshe, sanarwar ta ce sabon shugabancin hukumar zai fara aiki ne nan take domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara.