Daga BASHIR ISAH
Ƙungiya Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya, MOPPAN, ta miƙa saƙon taya murna ga sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Cikin sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa-hannun Babban Sakatare na Ƙasa, Salisu Muazu, MOPPAN ta ce a madadin mambobinta tana taya murna ga Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na sabon Gwamnan Jihar Kano.
A cewar ƙungiyar, nasarar Gwamna Abba nasara ce ga kowa a jihar Kano ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko makamancin haka ba.
MOPPAN ta nusar da Gwamnan kan cewa, alƙawarin sake gina Jihar Kano da ya yi wa al’ummar jihar na daga cikin manyan dalilan da suka sa aka zaɓe shi.
Don haka ƙungiyar ta ce tana fata Mai Girma Gwamna ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da kyakkyawan zaton da Kanawa suka yi masa wajen cika alƙauran da ya yi musu.
“Duk da dai aikin da ke gabanka babba ne, amma kyakkyawan fatan da ka samu daga sassan jihar ya ishe ka sauke nauyin da ya rataya a kanka ta yadda Kanawa za su yi alfahari da kai,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamnan da ya zama mai cika kalamansa sannan a ga canji na cigaba a sassan jihar a ƙarkashin gwamnatinsa.
Ta ce, “Hanya mafi dacewa ta yi wa Kanawa godiya dangane da wannan dama da suka ba ka, shi ne yin bakin ƙoƙarinka wajen cika alƙauran neman zaɓe da ka yi musu.
“Muna kira gare ka da ka zamanto na daban. An ɗora yaƙini da ƙwarin gwiwa mara iyaka a kanka, kuma muna fata ba za ka watsa mana ƙasa a ido ba.”