Wang Yi ya jaddada matsayin ƙasar Sin kan batun ƙasar Ukraine

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi ya bayyana a jiya Alhamis a birnin Tunxi dake lardin Anhui na gabashin ƙasar Sin cewa, ƙasar Sin ta taka rawar da ta dace kan batun ƙasar Ukraine.

Minista Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karin haske, kan matsayin ƙasar Sin game da batun ƙasar Ukraine, yayin wani taron manema labarai da aka shirya, bayan taron ministocin harkokin wajen ƙasashen dake makwabtaka da ƙasar Afghanistan karo na uku, da kuma taron ministocin harkokin waje na farko a tsakanin ƙasashen dake makwabtaka da Afghanistan da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Afghanistan.

Ƙasar Sin dai ta yi imanin cewa, tattaunawa da shawarwari, ita ce hanya daya tilo mafi dacewa wajen warware batun ƙasar Ukraine. Ya kara da cewa, ƙasar Sin ta yi kira da a tsagaita bude wuta tare da goyon bayan tattaunawa kai tsaye tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine.

Mai fassarawa: Ibrahim Yaya